Fahimtar juna ko soyayya: Wanne ginin aure ne ya fi ƙarko?

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Gabatarwa

Auren zamani na fuskantar barazana iri-iri. Sau da yawa muna jin “sun yi shekara biyu da aure, amma sun rabu” ko “aure ya tashi saboda rashin jituwa. “ta kasha mijinta alhali ita ta kawo shi ta ce “ta ji ta gani” “Satinmu biyu da aure amma ya fara faɗamin maganganu marassa daɗin ji” da sauran halaye da ma’aurata kan fuskanta kafin auren ya ci talata da laraba. Waɗannan lamura sun sa mutane da dama tambaya. Shin aure ya fi dorewa ne idan an fara da soyayya mai zafi, ko idan an gina shi bisa fahimtar juna? A cikin wannan nazari za mu zurfafa cikin wannan tambaya, tare da bayani bisa hujjoji da fahimta mai ƙarfi.

1. Auren soyayya: Idan zuciya kaɗai ke gudanar da rayuwa

Auren soyayya shi ne irin auren da aka shiga saboda ƙaunar da ke tsakanin masoya. Kalaman soyayya, kiraye-kirayen waya, da zumuɗin kasancewa tare suna daɗaɗa rai sosai. Amma duk da haka, idan aure ya dogara ne kawai akan wannan shauƙi to ga abin da yakan biyo baya.

Fuskantar rayuwa ta gaskiya

Soyayya za ta iya dusashewa da zarar an fara fuskantar  rayuwa ta gaskiya da gaske. Misali, biyan kuɗin haya, kulawa da cin kwalam da makulashe inda aka faro a gida , in an haihu kula da yara, kula da lafiya da kyale-kyale musamman a yau da ake kira da skin care, rage kullum ana makale da juna da kalmar nan ta caring ba a son a yi nesa ko da kuwa neman abinci za a je. Haka ɗaukar nauyin abin da aka san dole a gaji saboda ba za a iya ba. Waɗannan da ma wasu dalilai da dama na iya rage kuzarin soyayya.

Ba kowanne hali ne mai jure saɓani ba.

Soyayya zalla ba ta koyar da yadda za a magance rikici. Auren da aka fara da ƙauna, amma babu juriya, na iya rushewa da ƙaramin ƙorafi. Rashin fahimtar juna kan haifar da gajiyar zuciya. Idan babu dacewar hali, soyayya kan gaji saboda mutane na iya son juna, amma ba za su iya rayuwa tare cikin natsuwa ba.

2. Auren fahimtar juna lokacin da hankali ke gaba da zuciya

Auren da aka gina bisa fahimtar juna yana nufin ma’aurata sun karanci juna, sun gane halayensu, sun yarda da bambance-bambancen ra’ayi da tunani kafin aure. Wannan ya haɗa da:

Yin mu’amala da juna ba tare da kwaɗayi ba: Hakan yana ba da dama a ga ainihin halayen juna cikin gaskiya.

Tattaunawa akan muhimman batutuwa: Irin su kula da gida, kula da iyaye, yawan yara, tsarin kuɗi da sauran abubuwa waɗanda suke da tasiri a aure.

Karɓar juna yadda ake: Auren fahimta ba ya buƙatar a canza mutum, sai dai a jure masa ko a daidaita da shi.

Fahimta tana haifar da:

Girmamawa da mutunta juna

Sauƙin magance saɓani

Haɓakar soyayya a hankali

Zaman aure mai daɗi da ƙarko

A hakikanin gaskiya, soyayya tana da mahimmanci, amma ta gaskiya tana tasowa ne daga ayyuka da dabi’u. Fahimta ita ce ginshiƙi saboda ba kullum ne soyayya ke girma ba, amma idan akwai fahimta, soyayya na iya komawa cikin sauƙi bayan saɓani ko damuwa. Ma’aurata masu fahimta su kan fi jure rayuwa , su kan gane lokacin da ɗaya ke cikin damuwa ko jinkirin faranta rai, kuma su ba juna dama su dawo da kuzari ba tare da zargi ko cin fuska ba.

Kammalawa

Auren soyayya na da ɗanɗano da kuzari, amma ba shi da ƙarko idan ba a ɗora shi kan fahimtar juna ba. Auren fahimta kuwa yana iya fara da sauƙi, amma yana haifar da zurfin soyayya, zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa. Rayuwar aure tana da matakai kamar zaman farko da ake jin daɗi sosai.

Sai matakin fuskantar bambance-bambancen hali. Akwai matakin gwaji – lokacin da wasu daga cikin burin rayuwa ba su cika ba. Sannan matakin haƙuri da juna har soyayya ta girma ta gaskiya. A wannan tafiya, fahimta ita ce jagora. Soyayya na iya zama haske, amma fahimta ita ce fitilar da ke ɗaukar hasken har gaba.

By ukarofi