
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Duk dq cewa a kwanan nan aka kammala gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025, wasu daga cikin ‘yan wasan Super Eagles sun cigaba da nuna bajinta a ƙungiyoyinsu.
Yayin da wasu ‘yan wasan suke kan koma wa ƙungiyoyinsu, tuni wasu suka cigaba da haskawa bayan Super Eagles ta yi nasarar samun matsayi na uku a AFCON da aka gudanar a ƙasar Moroko.
Daga Italiya zuwa Turkiyya a gasar Champions League da Laliga, an ga yadda taurarin suke gwabzawa da abokan karawa a gasa da daban-daban.
Daga cikin waɗannan ‘yan wasa akwai Akor Adams mai shekaru 25, wanda ya yi ƙoƙari matuƙa a AFCON, wanda ya ci ƙwallo wa ƙungiyarsa Sevilla ta ƙasar Sifaniya bayan taimaka wa Nijeriya samun kyautar “bronze medal”.
Bayan zura ƙwallo uku da taimakawa aka ci huɗu, Ademola Lookman ya koma ƙungiyarsa ta Atlanta da ƙafar dama, inda ya taimaka aka ci ƙwallo ɗaya a wasan da suka yi rashin nasara a hannun Athletic Bilbao da ci 2 da 3 a gasar Champions League.
Haka ma Victor Osimhen, wanda ya koma ƙungiyarsa ta Galatasaray a wasanta na Champions League a ranar Laraba.
