Rumbun lantarki na ƙasa ya lalace karon farko a 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Juma’a ne Rumbun Lantarki na Ƙasa ya lalace a karon farko cikin shekarar 2026.

A cewar wani bayani da cibiyar gudanarwar ayyuka ta ƙasa (NISO) ta fitar, adadin raba wuta ya ragu zuwa megawat sifli.

Hakan ya faru ne daga ƙarfe 1 na rana, inda aka samu adadin wuta a kamfanonin raba wutar lantarki na DisCos ya sauka zuwa megawat sifli.

Kamfanonin sun haɗa da na yankunan Benin, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, Fatakwal, Ibadan, Abuja, da Yola.

A shekarar 2025, an samu lalacewar rumbun sau da dama, waɗanda na ƙarshensu shine wanda ya auku a ranar 29 ga watan Disamba.

Ana samun haka ne duk da gyare-gyaren da aka sha yi na inganta adadin samar da lantarki a sassan Nijeriya.

Akan haka ne Kamfanin Raba Lantarki na Neja-Delta ya ce ya samar da ƙarin megawat 450 ga masu amfani a wuta a yankunan da ke ƙarƙashinsa.

By Babaji