Kisan Kurmin Wali: An yaba wa Gwamna Uba Sani bisa ziyartar jama’ar ƙauyen

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An yaba wa Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa zuwa ƙauyen Kurmin Wali domin jajenta wa al’ummar yankin bisa garkuwa da mutanensu da ‘yan bindiga suka yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsere a yayin faruwar al’amarin ne suka yi jinjinar a ranar Juma’a inda suka jaddada goyon bayansu ga jagorancin gwamnan bisa ziyarar da kuma ba su kulawar lafiya da fadakar da su akan al’amuran yau da kullum.

Da yake ganawa da manema labarai, Mista Joseph Kurmin Wali ya bayyana yadda maharan siak farmake su a safiyar ranar Lahadi yayin da ‘yan yankin suke ibada a coci.

Ya ce, a yayin haka ne ‘yan bindigar suka umarci mutanen da su kwanta da fuskantar da fuskokinsu ƙasa gabanin tafiya da su cikin daji, yana mai cewa ya sami tserewa ne a lokacin da aka samu rikicewa daga ɓangaren maharan wajen tafiya da mutanen.

Musamman ya yabi Uba Sani bisa ziyartar Kurmin Wali a Ƙaramar Hukumar Kajuru domin jimami da duba matakin ɓarnar da harin ya yi.

Kazalika, ya yi wa gwamnan addu’ar cigaba da gudanrda jagoranci na gari a jihar da ƙoƙarin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’ummarsa.

By Babaji