Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bayanan Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa, darajar Naira ta ƙaru a kasuwar canjin kuɗaɗe ta hukuma a makon kasuwanci na uku na watan Janairun 2026, inda ta rufe a kan N1,417.95 kan kowace Dala.
Wannan sabon farashi na nuni da ƙaramar ci gaba idan aka kwatanta da makon da ya gabata, inda aka rufe kasuwa a N1,424.50 kan dala.
Hakan na nuna wani irin kwanciyar hankali a kasuwar canjin kuɗaɗe, duk da ci gaba da matsin buƙatar dala daga masu kasuwanci da masu shigo da kaya.
Bayanan CBN sun nuna cewa naira ta yi ta canjawa a cikin wani ƙaramin zango tsawon makon. A ranar Litinin ta buɗe a N1,425 kan dala, sannan ta ɗan inganta zuwa N1,420.25 a Talata, da N1,419.50 a Laraba, sannan ta ɗan koma N1,420 a Alhamis, kafin daga bisani ta rufe makon da ƙarin ƙarfi a N1,417.95 a Juma’a.
Masana harkar kuɗaɗe sun bayyana cewa wannan daidaituwar farashi na nuni da wani yanayi na tsaka-tsaki tsakanin buƙata da samuwar dala a kasuwar hukuma, inda ɓangarorin biyu ke taka tsantsan.
ƙarin ƙarfin da naira ta samu ya zo ne tare da ɗan tashin ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Nijeriya. CBN ta ce ajiyar kuɗaɗen ya rufe makon a dala biliyan 45.8, idan aka kwatanta da dala biliyan 45.6 da aka samu a makon da ya gabata.
Masana sun danganta wannan ƙarin ajiyar kuɗazen da ci gaba da shigar kuɗaɗen fitar da mai, da kuma dawowar jarin masu saka hannun jari na waje, wanda hakan ya taimaka wajen rage matsin lamba a kan naira.
Tun farkon shekarar 2026, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Nijeriya na nan sama da dala biliyan 45, abin da ke bai wa gwamnati kariya daga tasirin girgizar tattalin arzikin duniya, tare da taimakawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a kasuwar canji ta hukuma.
Duk da wannan kyakkyawan yanayi da aka samu a makon, masana na gargadi cewa har yanzu naira na fuskantar matsin lamba sakamakon yawan buƙatar dala a kasuwannin hukuma da na bayan fage.
Ana kallon kwanciyar hankalin naira a matsayin muhimmin ginshiƙi ga tattalin arziƙin Nijeriya baki ɗaya, musamman wajen rage hauhawar farashi, tallafa wa kasuwancin da ke dogaro da shigo da kaya daga waje, da kuma sauƙaƙa nauyin biyan bashin waje.
