Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya gana da shugabannin kamfanin simintin Ashaka ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Ibrahim Aminu, domin zurfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin, musamman a fannonin samar da ayyukan yi, kare muhalli da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Taron, wanda ya gudana a ranar Talata, ya mayar da hankali kan hanyoyin ƙarfafa haɗin kai wajen samar da guraben aiki ga matasa, kula da muhalli, faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, da kuma ci gaba da tallafa wa al’ummomin da ke karɓar baƙuncin masana’antar siminti.
A yayin tattaunawar, shugabannin Ashaka Cement sun sanar da gwamnan sabon sauyin mallakar kamfanin bayan sayen sa da kamfanin Huaɗin Cement na ƙasar China.
Darakta Janar ya bayyana cewa Huaɗin, wanda ke da tarihin fiye da shekaru 100 a harkar samar da siminti, zai kawo sabbin jarin zuba hannun jari, fasahohin zamani da kuma ƙa’idojin aiki na duniya zuwa siminti Ashaka.
Ya ƙara da cewa, sabon mamallakin kamfanin ya riga ya sanar da shirin faɗaɗa ƙarfin samar da siminti da ƙarin tan miliyan biyu a kowace shekara. A cewarsa, wannan shiri zai samar da ƙarin ayyukan yi, ya kara yawan kuɗaɗen shiga ga jihar, tare da bunƙasa ayyukan tallafin al’umma na kamfanin a yankunan da masana’antar ke aiki da ma faɗin jihar baki ɗaya.
Haka kuma, Darakta Janar ya bayyana cewa siminti Ashaka, wanda a halin yanzu shi ne mafi biyan haraji a yankin Arewa maso Gabas kuma babban mai ɗaukar ma’aikata a Gombe bayan gwamnati, na shirin ƙaddamar da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 16.
Ya ce, tashar, wadda ke da tanadin faɗaɗa nan gaba, za ta taimaka wajen rage matsalar wutar lantarki a cikin ayyukan kamfanin tare da bayar da gudunmawa wajen inganta samar da lantarki a jihar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan sabon salo na zuba hannun jari, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da Ashaka Cement domin cimma muradun bunƙasa da ci gaban jama’a.
Ya buƙaci kamfanin da ya kara zage damtse wajen kare muhalli, aiwatar da hakar ma’adanai mai ɗorewa, da kuma faɗaɗa shirye-shiryen tallafin al’umma da za su shafi kai tsaye al’ummomin da ke karɓar baƙunci da jihar baki ɗaya.
“Babban abin da ya fi damuna shi ne walwalar al’ummarmu, musamman mutanen da ke yankunan da masana’antar ke aiki. Dole ne su ji daɗin albarkatun da Allah ya basu ta hanyar ayyukan yi, kayan more rayuwa da kuma ci gaba mai ɗorewa,” inji gwamnan.
Ya kuma jaddada buƙatar gaskiya da riƙon amana, inda ya nemi a ƙara haɗa kai tsakanin Ashaka Cement da hukumomin haraji da tattara kuɗaɗe na jihar domin inganta musayar bayanai da tabbatar da tsarin samun kuɗaɗen shiga mai adalci da riba ga kowa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatar wa kamfanin da samar da yanayi mai kyau na kasuwanci, yana mai alkawarin cikakken goyon bayan gwamnatin jihar wajen inganta haɗin gwiwar da za ta haifar da ci gaban tattalin arziki, kare muhalli da bunƙasar jama’a.
Ya bayyana fatan cewa ƙarfafa dangantakar za ta samar da alfanu mai ɗorewa ga al’ummar Gombe, yankunan da ke karɓar baƙunci da kuma kamfanin kansa, tare da kara jaddada matsayin jihar a matsayin wurin da ke jan hankalin masu zuba hannun jari nagari.
A taron, gwamnan ya samu rakiyar Shugabar Hukumar Haraji ta Jihar Gombe, Hajiya Aisha Adamu.
