
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An jiyo harbe-harben bindiga da fashewar boma-bomai da ba a tabbatar da daga inda suke ba a daren Laraba wayewar Alhamis a Filin jiragen sama na birnin Niamey da je Jamhuriyar Nijar.
Majiyoyi daka ƙasar sun shaida wa masanin harkar tsaro, Zagazola Makama cewa an ga yadda yanayin filin ya kasancewa cikin matsanancin hali da harbin bindigu da tashe-tashen ababen fashewa.
A cewarsu, tuni hukumomin tsaro da na agajin gaggawa suka kwantar da hankalin jama’a a yankin, saidai har yanzu ba a gano waɗanda ke da hannu a ɗanyen aikin ba.
Zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, hukumomin Nijar ba su fitar da cikakken bayani game da faruwar iftila’in ba.
Haka kuma ba a san iya waɗanda al’amarin ya rutsa da su ba.
