Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa NHRC ta bayyana cewa ta saurari ƙararrakin cin zarafi miliyan 3.7 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja a shekarar 2025.
Shugaban Hukumar Tony Ojukwu ya sanar da haka yayin sa yake gabatar da ayyukan da hukumar ta yi daga Janairu zuwa Disamba ta 2025.
Ya ce kaso kaɗan ne daga cikin wanda hukumar ta saurara ne ta iya gudanar da bincike a kansu.
Wani babban mashawarci kan illar cin zarafin mutane na Hukumar Hiliary Ogbonna a ranar Talata ya ce Hukumar ta kammala gudanar da bincike kan ƙararraki 52,489 daga cikin miliyan 3.7 ɗin da ya samu.
Ogbonna ta ce hakan na da nasaba ne da rashin kuɗaɗen da hukumar ke buƙata domin gudanar da ayyukkanta yadda ya kamata.
A kwanakin baya ya ce Hukumar ta koka wa gwamnati kan kuɗaɗen da ake ware mata a kasafin kuɗin shekara basa isa ta gudanar da ayyukkanta yadda ya kamata.
A haɗaɗɗiyar kwamitin Majalisar dokoki da ta Wakilai yayin da yake gabatar da kuɗaɗen da aka ware wa hukumar a kasafin kuɗin shekarar na 2024 Ojukwu ya koka da ƙarancin kuɗaɗen da hukumar ke samu da ta kara yawan kuɗaɗen ta take ware wa hukumar.
Ojukwu ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara yawan kuɗaɗen da take ware wa hukumar musamman yanzu da aiki ke ƙara ƙaruwa wa hukumar.
A kasafin kuɗin shekara biliyan 8 ne gwamnati ta ware wa hukumar a 2025.
Ya yi kira ga manema labarai da su ƙara yawan kuɗaɗen daga aƙalla zuwa naira 19.55 daga biliyan 8 musamman yanzu da hukumar ke ci gaba da samun ƙararrkin cin zarafin a ofisoshinta.
Da aka duba kasafin kuɗin shekara gwamnati ta ware naira miliyan 8 wa hukumar.
Ya ce cin zarafin mutane na daga cikin laifukan da hukumar ta saurara inda samun ci gaba wajen yakan wannan matsala na dogaro ne da hada hannun da masu ruwa da tsaki.
“A shekarar 2025 NHRC ta samu ci gaba wajen yakan matsalar con zarafin mutane a dalilin hada hannun da ta yi da kungiyoyin Kare Haƙƙin dan Adam, sarakunan gargajiya da sauran mutane.
Ojukwu ya ce 2026 Hukumar za ta mai da hankali wajen gano alamun da ake fara ganowa wajen cin zarafin mutane sannan da ɗaukar matakan wajen kare mutane daga samun matsaloli irin haka.
Ya kuma ce hukumar za ta hada hannu da jami’an tsaro da hukumar shari’a domin samar wa wadanda aka ci zarafinsu kariya tare da tabbatar da an kwato hakkinsu ta shari’a.
Hiliary Ogbonna daga daga cikin mashawartan harkokin kare haƙƙin dan Adam na hukumar ya ce daga cikin ƙararraki miliyan 3.7 da hukumar ta saurara yankin Arewa wacce ta fi kowace yanki yawan kararrakin na da miliyan 1, 317, 213.
Ogbonna ya ce jihar Benuwe ce jihar da ta fi yawan kararrakin cin zarafin yara kanana a kasar nan.
