’Yar Nijeriya ta rasa lasisin aiki jinya a Australia kan yin barci a bakin aiki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya a jihar New South Wales ta ƙasar Australia ta soke lasisin wata ’yar asalin Nijeriya mai suna Chimzuruoke Okembunachi, bayan wata kotu ta gano cewa ta riƙa yin barci yayin da take bakin aiki a wani gidan kula da tsofaffi da ke birnin Sydney.

Kotun ta bayyana cewa halayen nata sun kai matsayin rashin ƙwarewar aiki mai tsanani, lamarin da ya iya jefa rayuwar marasa lafiya cikin haɗari.

A cewar hukuncin, matar mai shekaru 25 ta kasance ita kaɗai ce ma’aikaciyar jinya mai rijista da ke kula da tsofaffi kusan 100 a lokacin da take aikin dare.

Rahotanni sun nuna cewa ta fara aiki a cibiyar Hardi Aged Care da ke Guildford a watan Fabrairu na shekarar 2024, amma cikin ƙasa da wata guda aka dakatar da ita, kafin daga bisani ta ajiye aiki da kanta.

A cewar bayanan da kotun ta saurara, Okembunachi ta yi barci a wurin aiki sau shida a tsakanin ranakun 13 zuwa 27 ga Maris, 2024. A wasu daga cikin dararen, an ruwaito cewa wasu marasa lafiya sun rasa shan magungunan rage raɗaɗi na morphine da aka tsara musu, sakamakon rashin kulawa yadda ya kamata.

Binciken ya kuma gano cewa ta taba umartar wata ma’aikaciyar taimako ta bai wa mara lafiya magani alhali ba ta da izinin yin hakan, abin da ya ƙara dagula matsalar marasa lafiya a cibiyar.

Abokan aikinta ne suka fara tada hankalin shugabanni kan halayenta a ranar 27 ga Maris, wanda hakan ya janyo dakatar da ita washegari.

A gaban kotu, Okembunachi ta amsa laifukan da ake tuhumarta da su tare da nuna nadama. Ta bayyana cewa tana fuskantar matsalolin lafiya, matsin lambar karatu da kuma nauyin tallafa wa iyali ta fuskar kuɗi, wanda a cewarta ya jefa ta cikin gajiya mai tsanani. Sai dai kotun ta ce duk da gaskiyarta da nadamar da ta nuna, hakan bai kawar da hadarin da halayenta suka haifar ga rayukan marasa lafiya ba.

Kotun ta yanke hukuncin cewa soke rijistarta shi ne matakin da ya dace domin kare lafiyar jama’a, tare da hana ta neman a sake duba hukuncin na aƙalla watanni tara masu zuwa.

By ukarofi