Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta riga ta biya kuɗaɗen diyya na Naira miliyan 381 ga Mutanen da za ta yi amfani da wuraren su domin ginin hanyar da za ta zagaye garin Daura ta Yammaci, wato Western bye-pass.
Aikin hanyar ya ƙunshi gina tagwayen hanya da ta ta shi daga Ganga zuwa shatatalen cikin garin Daura mai tsawon kilomita 11.4, sai kuma faɗaɗa titin da ya haɗe titin Daura da Katsina, mai tsawon kilomita 3.2.
Kwamishinan ma’aikatar ƙasa da tsare-tsare, Dr. Faisal Umar Kaita ya miƙa chakin kuɗaɗen ga mutane 786.
Wannan biyan kuɗaɗen diyya zai amfani mutanen ƙananan hukumomin Daura da Mai’adua da aikin hanyar ya shafa.
Dr. Faisal Umar Kaita yace tagwayen hanyar na daga cikin ƙudirin gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa na faɗaɗa titunan manyan garuruwa, don magance ƙalubalen da ka iya tasowa.
Kwamishinan yace tuni gwamnatin Katsina ta sabunta taswirar wasu manyan garuruwa, ciki har da ƙaramar hukumar Daura, domin ya zama jagora ga tsara birnin na Daura.
Dr. Faisal ya yi nuni da cewar, aikin faɗaɗa titunan zai inganta tattalin arziki da rage cunkoso, yace gwamnatin Dikko Raɗɗa ba za ta gajiya ba wajen ayyukan da za su bunƙasa rayuwar al’umma a dukkan matakai.
Wasu daga cikin al’ummomin da suka amfana da kuɗaɗen diyyar sun yaba a kan biyansu, a kan lokaci.
Gwamnatin Shehu Shema ta fara aiwatar da irin wannan hanya a garin Katsina kafin shi kuma gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ƙara gina irin wannan hanya a Katsina da kuma wanda za a fara a Daura.
