Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar baƙuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC na ƙaramar hukumar Bakori a ofisoshin sa.
Ya sanar da cewa an saka ƙaramar hukumar Bakori cikin ƙananan hukumomin da za su amfana da aikin gina tagwayen hanyoyi a shekarar 2026.
Malam Dikko Raɗɗa ya ce gwamnati ta yanke wannan shawara ne saboda yawan chunkoson ababen hawa da matsalolin sufuri, da ake fuskanta a cikin garin, kuma hakan zai inganta sufuri, tsaro, da bunƙasa tattalin arziƙin yankin.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa na da aniyar inganta ababen more rayuwa tare da tabbatar da cigaba a dukkan ƙananan hukumomi.
Ya kuma yi alƙawarin duba sauran buƙatun da aka gabatar, tare da kira ga ‘ya’yan jami’yyar APC da su ƙarfafa haɗin kai tare da ƙoƙari wajen sabunta rijistar jam’iyya.
A ɗaya ɓangaren, shugaban masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar ta Bakori Farfesa Ahmed Muhammad, ya yaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin ke aiwatarwa a yankin, tare da roƙon gina babban asibiti da gyara manyan hanyoyi, musamman titin Bakori zuwa Guga, da Kakumi.
