
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Asusun bayar da lamunin karatu ga ɗaliban manya makarantu a Nijeriya (NELFUND), ya ce ya ƙara wa’adin yin rajistar neman aron kuɗi ga ɗalibai na zangon karatun 2025/2026 daga 31 ga Junairu zuwa 27 ga watan Fabarairu.
Daraktan yaɗa labaransa, Oseyemi Oluwatuyi ya bayyana a wata takarda, ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce, an yi haka ne da nufin bai wa wasu ƙarin ɗalibai damar yi da kuma kammalawa ga waɗanda suka fara ta yadda za a tabbatar da babu wanda aka bari a baya saboda matsalar da shafi rashin wadataccen lokaci.
Da yake jawabi akan matakin, Darakta Manaja na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, ya ce hakan ya nuna yadda asusun ke aiki tuƙuru wajen ganin ta bada ɗalibai masu yawa damar samun lamunin.
Ya kuma yi kira ga masu buƙata da waɗanda suka fara nema da su yi ƙoƙari kammala miƙa buƙatarsu daga yanzu zuwa ranar da sabon wa’adi zai ƙare.
Kazalika, ya ƙara da cewa, za a cigaba da yaɗa labaran NELFUND ta kafafen da suka amince da su a hukumance da kuma adireshin Imel kamar haka [email protected].
Kafafen sune: X(Twitter): @nelfund, Instagram: @nelfund, Facebook da LinkedIn: Nigerian Education Loan Fund – NELFUND da shafinsa na yanar gizo, wato www.nelf.gov.ng.
