Masanin kasuwar jari ya nemi a tsawaita wa’adin cika sabbin sharuɗɗan hukumar SEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Shugaban ƙungiyar Masana Kasuwar Jari ta Nijeriya (CMAN), Farfesa Uche Uwaleke, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin Hukumar Kula da Kasuwar Jari ta ƙasa (SEC) na tilasta wa kamfanonin da ke aiki a kasuwar jari ƙara jarinsu, yana mai cewa matakin na da matuƙar muhimmanci wajen kare masu zuba jari da kuma ƙarfafa ɗorewar kasuwar.

Uwaleke, wanda kuma shi ne Daraktan Cibiyar Nazarin Kasuwar Jari a Jami’ar Jihar Nasarawa, ya ce tsarin jarin da ake aiki da shi tun daga shekarar 2015 ya daina dacewa da yanayin tattalin arzikin yanzu, musamman la’akari da fazuwar darajar naira da kuma saurin bunƙasar fasahar hada-hadar kuɗi ta zamani (fintech).

A cewarsa, shirin ƙara jarin ya yi daidai da babbar manufar SEC ta kare masu zuba jari da kuma tabbatar da zaman lafiyar kasuwar jari na dogon lokaci. Ya jaddada cewa kasuwa mai ƙarfafa ginshiƙai na kuɗi ita ce kaɗai za ta iya jure girgizar tattalin arziki tare da kare muradun masu zuba jari.

Sai dai Farfesan ya yi gargaɗin cewa nasarar shirin za ta ta’allaƙa ne kan yadda za a aiwatar da wasu muhimman ɓangarori na tsarin, musamman wa’adin da aka bai wa kamfanoni domin su cika sabbin sharuɗɗan jarin. A halin yanzu, SEC ta tsara watan Yunin 2027 a matsayin ƙarshen wa’adi ga dukkan kamfanonin da abin ya shafa.

Ko da yake ya amince cewa wa’adin ya yi kama da yadda ake yi a ƙasashen duniya, Uwaleke ya nuna damuwa cewa lokacin ya zo daidai da zangon zaɓukan shekarar 2027 a Nijeriya, wanda a al’ada ke haifar da yanayin rashin tabbas a kasuwanni da kuma rage zuba jari.

Saboda haka, ya ba da shawarar a tsawaita wa’adin zuwa watan Disamban 2027 domin bai wa kamfanoni ƙarin lokaci da kwanciyar hankali wajen tara jarin da ake bukata.

Haka kuma, Uwaleke ya buƙaci SEC ta yi la’akari da banbancin da ke tsakanin tsarin kula da kuɗaɗen zuba jari na gargajiya da kuma na ba tare da ruwa ba, yana mai cewa dukkansu na da tsarin aiki da hadurra mabambanta, don haka bai kamata a tilasta musu sharuddan jari iri ɗaya ba.

Ya kuma gargaɗi hukumar da ta tanadi matakan kariya domin kauce wa wasu sakamako marasa kyau da ka iya tasowa, kamar raguwar yawan kamfanonin cikin gida da kuma taƙaita ayyukan kasuwar jari a jihohi, musamman a wajen Legas da Abuja.

A ƙarshe, masanin ya jaddada cewa idan aka yi la’akari da waɗannan shawarwari tun da wuri, shirin ƙara jarin zai taimaka matuƙa wajen gina kasuwar jari mai ƙarfi, wacce za ta iya kare masu zuba jari tare da tallafawa bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi