Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta danganta mummunan kisan da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a Kano da ƙaruwar matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda ta buƙaci a ɗauki matakan gaggawa na haɗin gwiwar al’umma domin daƙile wannan barazana.
Sakataren yaɗa labarai na ACF reshen Jihar Kano, Nasiru Yusuf Ibrahim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin.
Waɗanda aka kashe sun haɗa da Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida, lamarin da ya girgiza mazauna unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano a makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da aka gudanar a Kano ranar Lahadi, Shugaban ACF na Jihar Kano, Dakta Goni Faruk Umar, ya ce irin wannan ɗanyen aiki ba zai yiwu ba face idan wanda ya aikata shi na ƙarƙashin tasirin miyagun ƙwayoyi ko kuma yana da alaƙa da wasu ƙungiyoyi masu aikata laifi.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda al’umma ba su yi katsalandan ba a lokacin da lamarin ke faruwa, yana mai jaddada buƙatar farfaɗo da tsarin tsaron al’umma a matakin ƙasa.
A cewarsa, ya zama dole kowace unguwa ta fara kula da tsaron kanta ta hanyar haɗa kan shugabannin gargajiya, na addini da na al’umma domin sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a yankunansu.
Dakta Umar ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara tsaurara dokoki kan sayar da makamai tare da tabbatar da cikakken bayanin masu saye, sannan a samar da tsarin ɗaukar hoton yatsun mazauna domin sauƙaƙa gano masu aikata laifi.
Ya ƙara da cewa ACF, ta hannun shirin Awkat da tallafin AARNU, za ta bai wa matasa 1,000 rancen kuɗi marar ruwa na naira dubu ɗari kowannensu kafin ƙarshen watan Yuni domin rage zaman banza da ka iya jefa su cikin aikata laifi.
Shugaban na ACF ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro, musamman ’yan sanda da DSS, kan saurin kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
A nata ɓangaren, Daraktar Muryar Matan Arewa, Binta Mukhtar Shata, ta ce taron an shirya shi ne domin bai wa iyaye mata damar tattauna hanyoyin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro da ke addabar iyalai.
Ta nuna damuwa kan sauyin ɗabi’u a cikin al’umma, tana mai cewa yanzu har iyaye mata na jin tsoron ’ya’yansu. Ta buƙaci a hukunta masu laifi tare da tabbatar da adalci, tare da alƙawarin cewa ƙungiyar za ta rika shirya irin wannan taro duk shekara domin ƙarfafa tarbiyyar iyali.
Haka zalika, Babbar Sakatariyar LESPADA, Maryam Hassan, ta ce lamarin ya girgiza jama’a a ciki da wajen Kano. Ta jaddada cewa duk da ƙoƙarin gwamnati, dole ne al’umma su taka rawa musamman wajen yaƙi da shaye-shaye, domin a cewarta babu mai hankali da zai aikata kisan kai ba tare da tasirin miyagun ƙwayoyi ba.
Kungiyoyin sun bayyana bukatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, al’umma da ƙungiyoyin farar hula domin yaƙi da shaye-shaye da kuma dawo da tsaro da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
