Borno: Dakarun tsaro sun halaka Kwamandan Boko Haram, Abu Khalid a dajin Sambisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun Rundunar Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tare da wasu ‘yan ta’adda a Dajin Sambisa.

A cewar rahotanni, Abu Khalid, wanda shi ne maitaimakin shugaban mayaƙan, an halaka shi ne a wani atisayen shafewa da dakarun suka ƙaddamar a Arewa ta Gabas a ƙarshen mako.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), majiyoyi sun ce Khalid, wanda jagora ne a harkokin gudanarwar ƙungiyar, kisan shi ya haifar da gagarumin giɓi ga ayyukan mayaƙan acikin maɓoyarsu da ke sanannen dajin.

An gano cewa yana da hannu a kitsa hare-hare da samar da kayan yaƙi da kuma zirga-zirgar mayaƙan a sassan shiyyar, wanda kashe shi ya zama babbar nasarar ga ayyukan yaƙi da ta’addanci da sojoji ke yi a arewacin Nijeriya.

Haka kuma, wannan ci-gaba ya taimaka wajen ƙara wa dakarun ƙarfin nasara akan kwamandojin Boko Haram da ‘yan bindiga a shiyyoyin arewa uku.

Wasu daga cikin kashe-kashen ‘yan ta’addar sun haɗa da Kachalla Kallamua Sakkwato, Kachalla Balla a Kogi da Kachalla Damokulo a Zamfara.

By Babaji