A ci daɗi lafiya tare da dakon ƙididdiga 

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Karshen dai tuka-tuki, tik. Gwamna da muƙarrabansa sun fice daga NNPP da shirin sauya sheka zuwa APC. To, a matsayina na Dan Kano wanda ya baiwa wannan gwamnati gudunmuwa don ta ci zabe a 2019 da 2023, ina jin cewa lallai an ci Amana ta, tudu biyu. Na farko Gwamna, a tsammaninmu, ya gaza fuskantar matsalolin da Kano ke fuskanta tun da aka zabe shi, sannan kuma a yanzu ya ci amanar kuri’ar kanawa ta hayar kokarin komawa APC.

Saboda lalaci da lalacewa da al’ummar mu ta yi, za ka ga mutane wadanda su ka je makaranta (ta Boko da ta addini) su na hura hanci su na cewa wai Gwamna Abba na aiki. Saboda irin wannan zuga ta banbadanci ta zauna da gindinta, ya kasance kwakwalen wasu al’umma kama daga malamai, Yan siyasa, yan Boko da talakawa ke maye a cikin giyar wannan kirari. Hakan ne kuma ya sa shi kansa Gwamnan, saboda ya kewaye kansa da yan abi-yarima-a-sha-kida wadanda ba za su iya gaya masa tsagwaron gaskiya ba, ya fi kowa yarda da cewa ya na aikin, har ta kai ya yi shela a bara cewa ya cika duk alkawuran da ya daukar mana. 

Ni ina matukar kaunar wannan Gwamna domin ina kishin jiha ta da al’ummar jihar Kano, shi ya sa na bashi goyon bayan ya ci zabe da kyautata zaton zai ceto mu. Kuma a yanzu ma ina sukar kamun ludayinsa saboda kauna ba don kiyayya ba, da fatan Allah zai sa, kafin karshen wannan wa’adi ya gyara inda ya gaza kafin lokaci ya kure masa.

Mai karatu ka yi nazari da idon basira a kan hujjojin da zan bayar wadanda za su nuna maka cewa idan aka yi la’akari da yawan al’ummar jihar Kano (akalla mutum miliyan 16), da kudaden da wannan gwamnati ta karba a shekaru kusan uku (akalla Tiriliyan 1.3), da kasancewar manyan matsaloli na al’umma wanda wannan gwamnati ta gada, kuma ba ta iya magance su ba, hakika za ku fahimci cewa zancen Abba na aiki magana ce kawai ta banbadanci, siyasa ko jahiltar menene hakkin gwamnati a kan talakawanta.

Akwai manyan matsaloli da dama da su ka addabi jihar Kano, kama daga Ilimi, noma, lafiya, ruwan sha da ayyukan yi, don haka zan dauki guda daya tak, mu nazarce ta.

Ruwa, shine ginshikin rayuwa gaba dayanta, kuma shine ginshikin tattalin arziki har ma da zaman lafiya. Hasashen masana tun a shekarun baya ya nuna cewa kamar yadda a yau kasashen Duniya ke yake-yake saboda man fetur, nan da Yan wasu shekaru masu zuwa duk yake-yake za su rika faruwa ne sakamakon kokarin mallakar ikon ruwa tsakanin al’ummomi da kasashe. Ko mu a nan Najeriya, nan gaba zai wahala ba mu yi yaki da makwabciyar mu Nijar ba, a kan ikon kogin Kwara (River Niger) wanda a yanzu Nijar ta karya wata tsohuwar yarjejeniya da ta sahale mana basu wutar lantarki domin kada su yi madatsar ruwa a kan kogin Kwara, amma zuwan sojoji ya sa tuni Nijar ta fara Gina Dam a kansa. Haka kuma akwai wata rigimar a kwance tsakanin mu da Cameroon wajen ikon kogin Benue wanda ke janyo mana asara ta rayuka da dukiyoyi duk shekara sakamakon sakin ruwan dam ɗinsu.

Allah ya yi wa Kano ni’imar albarkatun ruwa, kama daga Dam-Dam 22 (ko mu ce 23 tunda a bara Gwamna Abba ya bada kwangilar Biliyan 6.7 don a gina sabon Dam a Kunci, yayinda wadancan ke barci). Sannan Kano na da rafuka da koramu da aka kiyasta sun Kai 100, wanda a ciki akwai manya guda 26. Wannan albarkatun na ruwa, idan da za’a yi aiki a kansu yadda ya kamata, jihar Kano za ta iya shayar da Afurka gaba daya da ruwan sha na shekaru (wato mutane biliyan 1.5).

A halin yanzu Kano na bukatar Lita miliyan 975 na ruwan sha a kullum, wanda matatar ruwa ta Challawa ke da capacity na Lita miliyan 200, ita kuma ta Tamburawa ke da Lita miliyan 150. Wato idan wadannan matatu na aiki a full capacity, Kano na bukatar wata Lita miliyan 400. Dam din Challawa Goje da ke da 969 million cubic sƙuare meters, idan za’a tsaida kwararar wani ruwa daga rafi ko ruwan sama ya sake shiga cikinsa, wanda ke kwance a cikinsa kawai, zai iya samar da gibin litre miliyan 400 da Kano ke bukata a kullum na tsawon shekaru 6.5 bai kare ba. Amma yanzu haka idan ka je wajen zaka ga spillway dinsa na malalar da ruwa cikin daji a banza na tsawon gomman shekaru. Wannan spillway zai iya samar da lantarki da ruwan noma na dubban kadada amma a banza ya ke kwaranya a daji (Kalli video na wannan spillway a nan: https://www.facebook.com/share/r/1UUiATivɗ6/ )
Matatar Tamburawa tun a lokacin Ganduje aikinta ya tsaya, dalilin da ya sa a yanzu hatta gidan Gwamnati da yankin Kumbotso, Tarauni da Nassarawa GRA su ka daina samun ruwa. A lokacin da wannan matata ta Tamburawa ke aiki, wallahi a gidana a Naibawa shower ce ke zuba 24/7.

A kokarin wannan gwamnati na samar da ruwa, sai ta bi gurguwar shawarar tafiya ta nemo bashi daga kasar Faransa har na biliyan 177 domin fadada matatar Tamburawa, maimakon ta fara maida hankali wajen farfado da samar da waccan Lita miliyan 150 da ta tsaya. Shin gwamnatin za ta tsaya tsakani da Allah wajen ganin an saka kudin inda aka nufa? Za ta iya gama aikin a lokacin ta?

Baya ga wadannan albarkatun ruwa da ke saman kasa (surface water) a matsayin Dam-Dam, koramu da rafuka, wata hanyar da a yanzu aka fi samun ruwan sha shine ruwan da ke karkashin kasa (wato underground water). Sakamakon gazawar amfanar ruwan da ke saman kasa, ya sa al’ummomi a ko’ina cikin fadin jihar sun raja’a wajen hako ruwa daga kasa, yadda a yanzu shi ke bada Kashi 85% na ruwan da jama’a ke amfani. Hakan na da illa nan gaba, domin ana ta zuke ruwan kasa, kuma yawan hakar borehole din na mummunar illa ga muhalli ta fuskoki da dama.

Jami’ar Bayero na fuskantar karancin ruwan sha a duk mazaunanta sabuwa da tsohuwa. Abinda ya sa wani kwamiti da aka kafa a shekarar 2022 na su Prof Salisu Dan Azumi, Dr Auwalu Lawan Yola, Arc Abdulmalik Aliyu Dikko da Engr Tukur Mohd Bulama, wanda su ka yi kokarin magance matsalar amma aikin na su ya tashi a banza saboda gazawar mahukunta a jami’ar da ita kan ta Gwamnatin jihar Kano. Wato abinda su ka yi shine na neman a farfado da wata matata da ke Challawa wadda ita ce ta farkon ginawa a Kano tun lokacin Sarki Abdullahi Bayero a shekarar 1933. Wato analog ce irin ta da can amma mai matukar inganci. Idan aka tashe ta, za ta iya samar da Lita miliyan 20, kuma ta na da bututu shi ma mai inganci irin na da wanda ya zo har BUK old site ya zarce ta kofar famfo wanda za’a iya kaishi New Site. Bayan kiyasi, wadannan masana sun bada shawarwari uku amma mafi saukin kashe kudi ita ce ta farfado da wannan matata a kan Naira miliyan 71. BUK na bukatar Lita miliyan Uku ta ruwa ne kacal a kullum, yayinda wannan matata za ta iya samar da Lita miliyan 20 a kan kudade miliyan 71. A cikin BUK akwai manyan boreholes da ke aiki guda 9 wadanda jumlatan su ke iya samar da Lita 600,000, wato kasa da kaso daya cikin uku na bukatar su. Amma hukumomin jami’ar da Gwamnatin Kano karkashin hukumar ruwa, su ka kasa dabbaka wannan aiki. Idan an farfado da wannan matata, baya ga BUK, duk yankunan Dorayi, Gadon-Kaya, Kabuga, Rijiyar Zaki da makwabta za su iya samun ruwa. To amma wani abin takaici shine, bayan gwamnatin ta gaza yin amfani da shawarar kwamitin, sai gashi watakila sakamakon aikin committee din ya nuna ashe matatar na da amfani har yanzu, sai wasu batagari kawai su ka je su ka wawashe ta.

A yanzu haka saboda karancin ruwa a BUK New Site, ta kai dalibai na yin Kashi a waje cikin Campus kamar Almajirai. A wannan yanayi da mahimman wurare irinsu BUK, unguwannin birnin Kano (har da GRA inda Gwamna ke zaune) ke karancin ruwan sha, maimakon a farfado da matatu irin wadannan da na Tamburawa, gwamnatin ta gwammace zuwa ta ciyo bashin biliyan 177 don a bada kwangilar fadada sabbin matatu a Tamburawa? Ba laifi bane yin sabbi domin cike gurbin bukatar ruwa da ake dada samu a kullum, amma ya gwamnati za ta shafe kusan wa’adinta ba tare da ta farfado da wadanda ake da su ba kafin ta dora? Nawa ne miliyan 71 da zai iya samar da ruwa Lita miliyan 20 ga al’ummomi da dama? Nawa ake kashewa wajen yawace-yawacen Gwamna, da gyara gine-gine irinsu ofisoshin ma’aikata da majalisa, saka fitulu a tituna, face-face da yin sabbin tituna, da gina sabon Dam akan 22 da ake da su? Don Allah duk wadannan ayyuka sun kai rabi-rabin samar da ruwan sha?

Idan ka dauki duk sauran sassa masu mahimmancin wadanda su ka shafi al’umma kai tsaye, kamar lafiya, Ilimi, noma da ayyukan yi, dukkansu a cikin irin wannan yanayi na harkar samar da ruwan sha su ke. Sannan saboda rashin tsoron Allah ace kowa ya zama Dan banbadanci ya rika cewa Abba na aiki? Ko dai aika-aika? Ya ya gwamnatin da a tarihi ta fi kowacce samun kudi amma kuma matsalolin mutanenta mafi mahimmanci an yi biris da su, sannan a rika cewa ai Gwamna na aiki?

Mu sani cewa da gwamnan, da ’yan kanzaginsa da masu cewa ya na aiki, da mu da kowa, wallahi za mu tsaya gaban Allah wata rana mu bayar da shaida. Mu gaya wa kanmu gaskiya, kuma mu gaya wa gwamna gaskiya, domin lokaci bai bar kowa ba. Kuma ya sani cewa, Allah ne ke bayar da mulki ya karɓe, yanzu idan aka kayar da shi zaɓe a 2027 (kamar yadda ta faru da Matawalle na Zamfara a 2023 bayan zaton cewa APC ke bada mulki ba Allah ba) zai ji cewa ya yi abinda muka ba shi amana? Mu dauka ma ya zarce wata shekara hudun, ya tuna Ganduje a 2019 da aka karbe zabe da karfin tsiya, yau ina Gandujen? Ya gama takwas din ya bar mulkin sannan Duniya na shaidar abinda ya shuka a shekaru takwas din, kafin a je babbar kotun Allah kowa ya bada ba’asi.

A ƙarshe kamar kullum shine kira ga al’ummar jihar Kano mu farfaɗo daga barcin da muke yi, kada mu bari koyarwar nan ta Aminu Kano ta na-ki wadda aka san mu da ita ta mutu. Mu ci gaba da cewa na-ƙi ga duk wata gwamnati da mu ka bata Amana ta ci. Tun daga jamhuriya ta daya har zuwa yanzu, Kano na kokarin bijirewa duk wata jam’iyya da bamu gamsu da kamun lidayinta ba. Kamar yadda muka ga bayan gwamnatin su Ganduje a 2023, yanzu an dawo mana ta bayan gida, yadda APC ta saka Lagos, Kano da Rivers a aljihu…to kuri’ar mu makamin mu ce ta kafa gwamnati ko kifar da ita. Mu ci gaba da lalube, mu na cewa na-ki, har ranar da Allah zai datar da mu da mutanen da za su dubi matsalolin al’umma ba na kashin kansu ba. Su Gwamna kuma da mukarrabansa, muna musu fatan a ci dadi lafiya, amma a zauna da shirin kididdiga, a nan Duniya (2027? ko 2031)… da kuma a gobe ƙiyama!

By ukarofi