Tsohon shugaban gyaran fansho na ƙasa, Abdulrasheed Maina ya yanki jiki ya faɗi a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An garzaya da tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho na ƙasa da aka mayar da shi Pension Reform Task Team a yanzu, wato Abdulrasheed Maina zuwa asibiti a ranar Talata sakamakon suma da ya yi a lokacin da yake ƙoƙarin shiga ofishinsa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a safiyar ranar a lokacin da Maina ya fara jin jiri da rashin ƙarfin jiki, kana daga bisani ya yanki jiki ya faɗi ƙasa.

Tuni ma’aikatan ofishin nasa suka garzaya da shi asibiti nan take domin ba shi agajin gaggawa.

Mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Emmanuel Nweke a wata takarda, ya ce likitoci sun ce yanayinsa ya daidaita bayan an ba shi kulawar da ta dace.

“Ya samu ɗan rauni ne sakamakon gajiya da matsin lamba, amma yanzu yana cikin kwanciyar hankali. Likitoci na ci gaba da sa ido kan lafiyarsa,” inji Nweke.

Zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ba a bayyana takamaiman asibitin da aka kwantar da Maina ba, saidai ana sa ran za a fitar da shi zuwa ƙasar waje nan da wasu ‘yan kwanaki yayin yake ƙara samun lafiya.

Maina ya shafe tsawon shekaru da dama yana fuskantar tuhume-tuhume akan zargin almundahana da sauya akalar kuɗaɗen fansho, wanda har yanzu ake gudanar da shari’a akan al’amarin nasa.

By Babaji