Daga UMAR GARBA a Katsina
Aƙalla mutum 21 ne suka mutu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya shaida wa manema labarai.
A tattaunawar sa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar, Surajo Aliyu Daudawa, ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutanen ne a matsayin ramuwar gayya bayan kashe wani nasu da aka yi a yankin duk da cewa an yi sulhu da su kusan watanni biyar da suka wuce.
“Mazauna yankin sun wayi gari cikin tashin hankali bayan harin, duk da cewa kafin hakan ba a fuskanci wata matsala ba tun bayan yarjejeniyar sulhu da aka yi da ‘yan bindigar.” in ji shi
Shugaban ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 21, amma babu wanda aka sace.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yi niyyar tafiya da mata, amma shugabanninsu suka hana hakan, suna mai cewa “ba sace-sace ne ya kawo su ba, illa ramuwar gayya.”
Da BBC ta tambaye shi abin da ya jawo maganar ramuwar gayya bayan an yi sulhu, Daudawa ya ce “kwana biyar kafin harin, an samu labarin cewa an sace mutane biyu tare da ƙwace babur guda ɗaya, sai aka tuntuɓi ‘yan bindigar kamar yadda yarjejeniyar sulhun ta tanada domin su taimaka wajen bincike.”
“Daga baya aka gano cewa mutanen biyu suna gidajensu, amma aka tarar da gawar ɗaya daga cikin Fulanin dajin da suka je taimaka musu neman mutanen, abin da ya jawo zargin cewa hakan ne ya hadassa harin.” In ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa an riga an yi jana’izar mutanen da aka kashe a garin Doma, yayin da al’umma ke kira ga hukumomi da su ɗauki matakan da za su hana sake faruwar irin wannan hari, musamman bayan an yi sulhu da nufin dawo da zaman lafiya a yankin.
