Tsohon Gwamnan Benuwai, Gabriel Suswam ya koma APC bayan barin PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai, Sanata Gabriel Torwua Suswam, ya fice daga Jam’iyyar PDP a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen zamansa na tsawon lokaci acikinta bayan shafe shekaru da dama.

Haka kuma ya sanar da komawarsa jam’iyya mai mulki, APC.

Suswam, wanda ya shugabanci jihar Benuwai a tsakanin shekarar 2007 da 2015, sannan daga bisani ya yi sanata a Majalisar Dattawa, ya miƙa takardar murabusa ɗinsa daga PDP ga Shugaban jam’iyyar na yankin Mbagber da ke Ƙaramar Hukumar Logo a yau Laraba.

A wata takarda da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Bartholomew Bede, tsohon gwamnan ya bayyana godiyarsa bisa damarmakin da jam’iyyar ta ba shi ciki har da daga darajarsa daga ɗan majalisar wakilai zuwa riƙe muƙaman gwamna da sanata.

Ya kafa hujja da ƙamarin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a matsayin dalilin ficewarsa acikinta, yana mai cewa babu wani matakin sulhu da aka ɗauka wajen shawo kan matsalolinta.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, duk da kwamtocin sulhu da shiga tsakani da aka sha yi, jam’iyyar ta gaza magance matsalolin da ke haddasa rikicin jagoranci, tsare-tsare da horo acikin ‘ya’yanta.

Akan hakan ne ya ce ya ga dacewar ɗaukar matakin nasa domin ci-gaban siyasarsa, yana mai yi wa tsohuwar jam’iyyar tasa fatan alkhairi.

By Babaji