Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta kammala kama wa maniyyatan Nijeriya a Hajjin 2026 masaukai a Makkah da Madinah, gabanin wa’adin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmed Mu’azu, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an samu nasarar saka bayanan masaukin Nijeriya tare da amincewar Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, bisa bin jadawalin da aka tanada.
Wannan ya biyo bayan umarnin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya buƙaci a kammala muhimman shirye-shiryen Hajji cikin wa’adin da Saudiyya ta saka, domin kare muradun Nijeriya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada buƙatar bin ƙa’idoji da lokaci domin kauce wa matsaloli a yayin gudanar da aikin Hajji.
Farfesa Usman ya yaba da goyon baya da shawarwarin mataimakin shugaban ƙasa, tare da nuna rawar da kwamitin NAHCON, tawagar manyan jami’ai da aka tura Saudiyya, Nusuk Masar, shugabannin Hukumar Jin daɗin Alhazan Jihohi, ma’aikatan NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki suka taka wajen kammala wannan aiki.
“Da kammala wannan tsari, Nijeriya ta riga ta tabbatar da masaukin maniyyatanta na Hajjin 2026, kuma tana cikin ƙasashen da suka cika wannan muhimmin sharaɗi cikin wa’adin da aka tanada,” inji sanarwar.
NAHCON ta ce yanzu ta shiga mataki na gaba na shirye-shiryen gudanar da Hajjin 2026.
