Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Iskar guguwar siyasa dai ta soma kaɗawa a Jihar Kebbi, sai dai a wannan karon siyasar za ta zo da sabon salo saboda yanzu gabar cikin gida ce ke neman ruguza jamiyyar APC mai mulki sanadiyyar neman kujeru musamman a matakin tarayya da suka haɗa da Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
A duk lokacin da mutane fiye da ɗaya ke neman abu ɗaya kuma kowannen su yana iya ɗaukar kowane mataki don cimma burin sa ba shakka akwai gumurzu.
Yanzu haka dai tirka-tirkar neman samun tikitin in zama ɗan takarar kujerar dan majalisar dattawa don wakiltar gundumar Kebbi ta tsakiya ta kunno kai tsakanin tsofaffin gwamnonin jihar da suka haɗa da Sanata Adamu Aliero wanda ya yi gwamnan jihar a farkon dawowa da dimokuraɗiyya a Nijeriya shekarar 1999 zuwa 2007, tsohon Ministan babban birnin tarayya a lokacin marigayi Umaru Musa Yar Adua kuma wanda yanzu haka shi ne ke kan wannan kujerar da kuma Sanata Atiku Bagudu wanda shi ma tsohon gwamnan jihar Kebbi ne da ya jagoranci jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023, kuma tsohon Sanatan da wakilci gundumar Kebbi ta tsakiya lokacin Umar Musa Yar Adua wanda yanzu haka shi ne Ministan kasafi da tattalin arziki.
Waɗannan gaggan yan siyasa dai kowanne ya ja daga da shi da magoya bayan sa har sai sun ga abinda ya ture wa Buzu naɗi kan neman wannan kujerar a zaɓen shekarar 2027.
Bangaren Sanata Adamu Aliero da na Sanata Atiku Bagudu sun daɗe suna yi wa juna kallon uku saura kwata tun lokacin da Atiku Bagudu yana gwamnan jihar Kebbi.
Dangantakar ta ƙara tsami a wannan lokacin da kowanen su ke da burin zama Sanata don wakiltar wannan mazaɓar ta Kebbi ta tsakiya bayan kowannen su ya yi gwamna ya yi Minista ya kuma yi Sanata saboda haka yanzu kowannen su yana so ne ya cigaba da zama ɗan Majalisar Dattawa har illa Masha Allahu wanda kuma kowanen su yana ganin idan ba shi ne ba, ba zama lafiya.
Sai dai a baya-bayan nan wara sabuwa ta fito inda waɗansu bayanai na nuni da cewa akwai yiyuwar ana kitsawa Sanata Atiku Bagudu gadar zare saboda Sanata Adamu Aliero ya nuna amincewa da dukkan su su haƙura da takara a 2027 a bar wa Surukin Gwamna Malam Nasir Idris wanda shi ne shugaban hukumar agajin gaggawa (MD NAMA) Injiniya Ahmed Umar Faruk bisa ga zummar idan gwamnan ya kammala zango na biyu a kan mulki a 2031 ya karɓi takarar Sanata saboda hasashen Aliero yana da faɗa a wajen shugaba Tinubu shi kuma idan ya bar Sanatan ana iya ba shi Minista yayin da shi kuma Sanata Atiku Bagudu ya kama tashar iska, wanda magoya bayan Sanata Atiku Bagudu su kuma su ke ganin wata yaudara ce aka kitsa wa mai gidan su.
Waɗansu daga cikin magoya bayan Sanata Atiku Bagudu suna ganin lokaci ya yi da Sanata Adamu Aliero ya kamata ya tsaya ya huta haka saboda yana cikin mulkin dimokuraɗiyya tun shekarar 1999 da aka dawo mulkin farar hula.
Alhaji Muhammed Aliyu yana daga cikin magoya bayan Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana cewa tun lokacin da aka dawo mulkin dimokuraɗiyya Sanata Adamu Aliero ya ke cikin daular siyasa l, ya yi gwamna ya yi Minista kuma yanzu shi ne Sanata da ke wakiltar gundumar Kebbi ta tsakiya.
Aƙalla daga shekarar 1999 zuwa yanzu shekaru ashirin da bakwai (27) kenan wanda ana iya a haifi mutum har ya yi firamare ya yi Sakandare ya yi Digiri ya yi aure har ya haifu a ce duk mutum ɗaya yana nan zaune a kan mukamin siyasa.
Maganar gaskiya wannan ba aikin hankali ba ne. Bisa ga ma’auni na hankali ya kamata a ce irin wadannan mutanen yanzu suna gidajen su zaune yan siyasa da sarakuna suna neman shawarwari gurin su.
Wata mai kama da wannan ita ma kujerar Dan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Bunza da Kalgo da kuma Birnin Kebbi babban birnin jihar tana fuskantar tankiya inda a halin yanzu ana rade-raden cewa wanda ke kan ta Honarabul Muhammed Bello Yakubu dan Jam’iyyar PDP ne da ake sa ran zai dawo Jam’iyyar APC tare da neman auren daya daga cikin yayan gwamnan jihar Malam Nasir Idris saboda samun sake dare kujerar a karo na biyu wanda kamar yadda masana siyasar Nijeriya ke cewa “za a yi Tuwo-na-mai-na”.
A ɗaya ɓangaren kuma akwai Dokta Usman Muhammed Tunga shugaban Kwalejin tarayya ta Kimiya da kere-kere da ke Birnin Kebbi wanda na hannun dama kuma ɗan gaban goshin gwamna Nasir Idris ne shi ma an bayyana cewa ya yunƙuro da zummar neman wannan kujerar ko ta halin yaya.
Sai kuma tsohon dan majalisar wakilai kuma shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Kebbi (SEMA) Honarabul Bello Yakubu (Rilisco) wanda shi ma a shirye ya ke da ya yaki duk wani Dan takarar wannan kujerar, wanda kuma yana da goyon bayan matasa da ‘yan siyasa da a ke ganin rasa wannan kujerar na iya sa ya fice daga jam’iyyar APC da zai illata ta ba kaɗan ba.
Haka zalika, shi ma shugaban hukumar alhazzai kuma babban jigo a siyasar jihar Kebbi wanda ya yi uwa da makarɓiya a zaɓen 3023 wajen ganin gwamna Malam Nasir Idris ya sami nasara tun kama daga lokacin zaɓen fitarda gwani har zuwa zaben game-gari yana daga cikin waɗanda ke da shawar takarar wannan kujerar a zaɓe mai zuwa wanda shi ma hana shi takarar kujerar yana da hatsari a wajen APC ba ƙarami ba.
Yanzu haka dai wannan yana daga cikin abubuwan da ke barazana ga samun haɗin kan yayan Jam’iyyar APC a Kebbi wanda yana iya sanadiyyar tarwatsewar Jam’iyyar saboda kowane ya ja daga da shi da magoya bayansa.
Kwanan nan dai gwamna Malam Nasir ya bayyana cewa duk wanda bai kyautatawa al’ummar da suka zaɓe shi ba ya koma Abuja ya yi kwanciyarsa, ba zai sake ba shi damar zarcewa ba, wanda ya sanya al’ummar jihar musamman ’yan siyasa nunawa juna yatsa.
Yanzu dai kamar yadda jam’iyyun adawa ke jira shi ne abinda ke iya biyowa bayan kammala gangamin babban taron Jam’iyyar APC nan gaba kaɗan da za a gudanar a matakai daban-daban.
