Adamawa: An kama wani mutum da ake zargi da sace mahaifinsa don karɓar kuɗin fansa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na cikin gida, ta kama wani mutum tare da wasu biyu bisa zargin sace mahaifinsa na jini a ƙauyen Jera da ke Gundumar Malabu, ƙaramar Hukumar Fufore.

Mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Yola.

Ya ce an samu nasarar cafke mutanen ne sakamakon ci gaba da yaƙin da rundunar ke yi da laifukan sace mutane da sauran munanan laifuka, ta hanyar ayyukan tsaro da suka dogara da bayanan sirri.

“Biyo bayan sabbin ayyukan sace-sacen mutane da suka kai ga sace Alhaji Ahmadu a Malabu a ranar 30 ga Janairu, kuma bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Morris Dankombo, na ƙara tsaurara matakan yaƙi da ’yan ta’adda,

“An gudanar da wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin jami’an ’yan sanda da mambobin Miyetti-Allah a wata maboyar da ake zargin ’yan sace mutane ke amfani da ita a ƙauyen Jera, Gundumar Malabu, ƙaramar Hukumar Fufore,” in ji shi.

A cewarsa, a yayin aikin, jami’an tsaro sun kama Lawali Haruna mai shekara 45, Yahaya Ibrahim mai shekara 25, da Da’u Alhaji Ahmadu mai shekara 28, dukkansu mazauna ƙauyen Jera a ƙaramar Hukumar Fufore.

“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ɗan mahaifin wanda aka sace ne na jini. Dukkan su ukun sun amsa hannu a cikin aikata laifin,” in ji Nguroje.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙari domin ceto wanda aka sace ba tare da ya ji rauni ba, tare da kamo sauran mambobin ƙungiyar masu aikata laifin. Ya ce a halin yanzu waɗanda aka kama suna tsare yayin da bincike ke gudana.

Nguroje ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda ya yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin rundunar ’yan sanda da jami’an tsaro na cikin gida, tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihin bayanai a kan lokaci domin taimakawa yaƙi da aikata laifuka a jihar.

By ukarofi