Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta yi gargaɗin cewa za ta iya jagorantar zanga-zangar gama-gari ko ma ƙauracewa zaɓe, sakamakon abin da ta kira ruɗani da saɓanin bayanai daga Majalisar Dattawa kan gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, musamman batun watsa sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki.
A wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar, ƙungiyar ta ce rashin fayyace matsayar da Majalisar Dattawa ta ɗauka kan ko za a wajabta watsa sakamako kai tsaye ta na’ura ya jefa shakku cikin tsarin zaɓe da kuma amincewar jama’a.
NLC ta ce, rahotannin da ke yawo sun nuna cewa kudirin da ya bukaci a tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, INEC, watsa sakamakon zabe kai tsaye daga rumfunan zaɓe zuwa dandalin IReɓ bai samu amincewa ba, inda aka bar tsohon tanadi da ke bai wa hukumar damar zaɓar yadda za ta watsa sakamakon.
A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya haifar da fargaba a faɗin ƙasa, kuma bayanan da suka biyo baya daga Majalisar sun kara rikitar da al’amura maimakon kawar da shakku. Ta kara da cewa a irin wannan lokaci mai muhimmanci bayan zaɓukan 2023, duk wata dokar da ta bar giɓi na iya ƙara gurgunta sahihancin zaɓe.
ƙungiyar ta buƙaci Majalisar Dattawa da ta fito da cikakken bayani a hukumance, ba tare da wata ruɗani ba, kan ainihin tanadin da aka amince da shi da kuma dalilan cire wajabcin kalmar “kai tsaye” a batun watsa sakamako.
NLC ta jaddada cewa ya kamata dokar da za a amince da ita ta wajabta wa INEC watsa da tattara sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kai tsaye daga rumfunan zaɓe, domin tabbatar da gaskiya da amincin tsarin dimokuraɗiyya.
Ta yi gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo matakin gaggawa daga ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa kafin, lokacin ko bayan zaɓe, har ma da ƙauracewa zaɓen gaba ɗaya.
Wannan gargaɗi ya biyo bayan amincewar Majalisar Dattawa da ƙudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2026 a karatu na uku a ranar 4 ga Fabrairu, 2026. A yayin amincewa da ƙudirin, majalisar ta yi watsi da shawarar da ta nemi a wajabta watsa sakamakon kai tsaye, inda ta bar tanadin da ke cewa a riƙa watsa sakamako “ta hanyar da hukumar ta tsara.”
Matakin ya jawo suka daga jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula, waɗanda ke ganin cewa komawa ga tarawa ta hannu na iya buɗe ƙofar maguɗi gabanin zaɓukan 2027.
Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce majalisar ba ta soke watsa sakamakon ta lantarki ba ne, illa dai ta cire kalmar “kai tsaye” domin kauce wa matsalolin doka da na fasaha. Ya ce an bar wa INEC sassauci ta zabi hanyar da ta fi dacewa bisa la’akari da ƙalubalen sadarwa da tsaro.
Duk da ce-ce-ku-cen, ƙudirin gyaran dokar ya ƙunshi wasu sabbin tsare-tsare kamar amfani da lambar ƙR wajen tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma kara tsauraran hukunci kan laifukan zaɓe.
