Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Tattara Shara da Kula da Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB), tare da haɗin gwiwar Kotun Tafi-da-Gidanka ta Tsaftar Muhalli, sun kulle ma’adanar man fetur ta Kamfanin Man Fetur ta Nijeriya (NNPC) da ke Hotoro, bayan samunta da laifin karya dokokin tsaftar muhalli.
Matakin, wanda aka ɗauka a ranar Alhamis, ya shafi muhimman wurare a faɗin jihar, ciki har da hukumomin gwamnati, cibiyoyin kasuwanci, kamfanoni masu zaman kansu da kuma banɗakunan wajen gidaje. Hukumar ta ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na tabbatar da bin dokokin tsafta domin kare lafiyar al’umma.
Daraktan REMASAB, Muhammad Khalil, ya bayyana cewa dokokin tsaftar muhalli ba wai don tsangwama ba ne, illa don kare rayuka da tabbatar da ingantaccen yanayi mai tsafta ga mazauna jihar. Ya jaddada cewa duk wanda aka samu da saɓa doka, ko mutum ne ko ƙungiya, zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
A yayin sintirin, an tarar da wani banɗaki a kan titin Hotoro cikin ƙazanta, lamarin da ya sa kotun ta ci tarar masu kula da wurin. Amma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne kullen ma’adanar NNPC da ke Hotoro, bayan an tabbatar da saɓa ƙa’idojin tsafta.
Haka kuma, a unguwar Naibawa kusa da Royal City, an kulle wani gini da ake ginawa sakamakon zuba yashi da duwatsu a kan titin jama’a ba bisa ƙa’ida ba, abin da ya hana zirga-zirga tare da jefa masu amfani da hanya cikin hadari. Kotun ta kuma ci tarar wanda ya aikata laifin. Irin wannan saɓa wa doka an sake samu a kan titin IBB Way, inda aka hukunta wani da laifin zubar da kayan gini a kan hanya.
Shugaban REMASAB ya yi kira ga mazauna Kano da su ɗauki tsaftar muhalli da muhimmanci, yana mai cewa bin doka wajibi ne, domin tsafta alhaki ne na kowa da kowa. Ya kuma yabawa Kwamishinan Muhalli, Dahir Hashim, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da suke bai wa shirye-shiryen farfaɗo da muhalli da ƙawata birane a jihar.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sintirin duba tsafta a faɗin Kano, domin ƙarfafa bin dokoki, kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsafta mai ɗorewa a al’umma.
