Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Rijistar Kamfanoni ta ƙasa (CAC), ta ce a yanzu tana karɓar kusan buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kowace rana, sakamakon fara amfani da fasahar ƙirƙirar basira ta zamani, wato Artificial Intelligence (AI), a ayyukanta.
Babban Magatakardan Hukumar, Hussaini Magaji, ne ya bayyana hakan yayin laccar bikin cika shekaru 35 da kafa CAC, wanda aka gudanar a ranar Litinin a Abuja.
Magaji ya ce, amfani da AI ya ƙara wa hukumar ƙarfi wajen sarrafa ɗimbin buƙatun rijistar kasuwanci da kuma tambayoyin kwastomomi da ke shigowa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
A cewarsa, adadin masu neman rijistar kasuwanci ya karu matuƙa sakamakon sauye-sauyen dokokin haraji, manufofin gwamnati na karfafa shigar da kananan sana’o’i cikin tsari na hukuma, da kuma bunƙasar kasuwancin da ke gudana ta kafafen sada zumunta da fasahar zamani.
“Yanzu CAC na karbar kusan buƙatun rijistar kasuwanci 10,000 a kullum, sabanin daruruwan da ake samu a baya. Haka kuma tsarinmu na karɓar matsakaitan tambayoyi 5,000 a rana ta hanyar imel da cibiyoyin kiran waya,” inji shi.
Ya bayyana cewa ba zai yiwu a iya tafiyar da irin wannan adadi ta hanyar tsoffin hanyoyin aiki na hannu ba, yana mai jaddada cewa AI ta zama ginshiƙi wajen wara sauri, daidaito da ingancin aiki.
Magaji ya ce tun daga ofishin hannu guda daya da aka kafa a Abuja a shekarar 1991, CAC ta rikide zuwa cikakkiyar hukuma ta zamani mai amfani da tsarin dijital daga farko har ƙarshe, wadda ke bayar da ayyuka a ko’ina cikin duniya cikin awanni 24.
Duk da ƙalubalen da aka fuskanta a farkon sauya tsarin zuwa sabon portal mai amfani da AI a shekarar 2025, Magaji ya ce sauye-sauyen sun fara haifar da sakamako mai kyau. Ya kuma gode wa masu ruwa da tsaki da kwastomomi kan haƙurin da suka nuna yayin wannan sauyi, yana mai tabbatar da wudurin hukumar na samar da ayyuka masu inganci irin na ƙasashen da suka ci gaba.
Haka zalika, ya sanar da ƙulla haɗin gwiwa tsakanin CAC da kamfanin Google domin kara karfafa tsarin fasahar hukumar da inganta saukin gudanar da kasuwanci a Nijeriya. A cewarsa, haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙara inganta aikin mahajar, tabbatar da ɗorewar tsarin da rage lokacin da ake dauka wajen kammala ayyuka.
Magaji ya ƙara da cewa CAC ta ɓullo da sabbin kayayyakin AI a shafinta na yanar gizo da aka sabunta, ciki har da mataimakin lauya na AI da ke amsa tambayoyin dokoki, da kuma na’urar kirkirar sunan kasuwanci domin sauƙaƙa ajiyar suna.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin Kasuwanci na Majalisar Wakilai, Ahmed Munir, ya yi alƙawarin bai wa hukumar goyon bayan majalisa domin kara bunƙasa ginshiƙin fasahar dijital, gaskiya da ƙirƙire-ƙirƙire.
Shi ma Darakta-Janar na Hukumar Raya Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA, Kashifu Abdullahi, ya tabbatar da shirin bai wa CAC cikakken goyon bayan fasaha wajen aiwatar da sauye-sauyen AI cikin nagarta da bin ƙa’idojin da suka dace.
