Kano: An yi asarar sama da biliyan N8, yayin da mutane bakwai suka yi ɓatan dabo a gobarar Singa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata gobara da aka yi a shararriyar kasuwar Singa da ke cikin garin Kano ta lalata kadarori da jimillar adadin kuɗinsu ya kai kimanin Naira biliyan 8.

Wannan al’amari ya yi sanadiyyar lalata sama da rassan kasuwanci guda 1,000 tare da ɓatan dabo da wasu mutane bakwai a sanadiyyar faruwar iftila’in.

Shugaban kasuwar, Junaid Zakari da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi, ya bayyana al’amarin a matsayin wanda ya jefa ɗaruruwan iyalai cikin ƙunci.

A cewarsa, gobarar ta ƙone manyan gine-gine guda huɗu da ke cikin kasuwar, waɗanda galibinsu aciki ƙananan ‘yan kasuwa suke gudanar da sana’o’insu.

Ya ce, kayayyaki da wasu abubuwa masu daraja sun ƙone ƙurumus, wanda ya ya yi sanadin lalata harkoki zuba jari na tsawon shekaru da jefa ‘yan kasuwa a halin rashin tabbas.

Haka kuma ya ce, mutane bakwai sun ɓata, inda tuni aka shiga gudanar da bincike daga ɓangare jami’an bada agajin gaggawa domin gano halin da suke ciki a raye ko mace.

A halin da ake ciki wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun koma wurarensu domin ɗauko ababen da suka rage da wutar ba ta ƙone ba.

Wani mai suna Isa Abubakar ya ce ya yi asarar sama da kayan miliyan N200 a gobarar, kamar yadda wani mai Musa Ibrahim ya ce shi ma ya rasa na sama da miliyan N340 cikin alhini.

By Babaji