Muƙamin da Gwamna Sule ya ba ni ba shi da alaƙa da siyasa – Ɗanmalikin Masaka

Spread the love

Daga JOHN WADA a Keffi

Wani matashi wanda gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa muƙamin mai taimaka masa na musamman a kwanan nan wato, Basiru Umar yace muƙamin bai da alaƙa da harkar siyasa kamar yadda wasu ke tunani.

Ɗanmalikin Masakan Basiru Umar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida ciki har da wakilin mu a gidansa da ke Masaka a ƙaramar hukumar Karu kwanaki kaɗan bayan karramawar da gwamnan ya yi masa.

Yace a matsayin sa na mai wannan sarautar Ɗanmalikin Masaka da ya daɗe yana tare da mai martaba sarkin Masaka (mai martaba Bisalla) yana kuma masa biyayya ɗari bisa ɗari, tsakanin sa da ‘yan siyasa sai dai ya yi musu fatan alheri da basu shawarwari na cigaban al’ummar jihar ta Nasarawa da Najeriya gaba daya. Ya ƙara da cewa ya tabbata hakan anyi masa ne sakamakon gudumawar da yake bai wa masarautar ta Masaka kasancewar suna tare da mai martaba sarki.

Dangane da shawara da yake da shi ga sauran ‘yan uwansa matasa sai Ɗanmalikin Basiru Umar yace” a kowanne lokaci shawara da muke bai wa na ƙasa damu shine a zauna lafiya don idan ana zama lafiya ba ƙaramin albarkatu ake samu cikin al’umma ba.

Har ila yau da yake tsokaci a kan batun sabon wani naɗin da shugaba Tinubu yayi wa sarkin Baka da ke yankin nasu na Karu a jihar wato na Ambassadar zaman lafiya na shiyar Arewacin ƙasar nan ta tsakiya, Danmalikin yace tabbas sarkin Bakan ya cancanci muƙamin idan aka yi la’akari da gagaruman gudumawa da ya daɗe yana bayarwa wajen cigaban yankin da jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Daganan sai Ɗanmalikin Masaka Basiru Umar ya kuma yi amfani da damar inda ya mika godiyar sa na musamman ga gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da karramawar da ya yi masa da muƙamin na mai taimaka masa na musamman, inda ya yi alƙawarin sauke nauyin da ke wuyan sa yadda ya dace sa’anan ya jinjina wa duka abokan arziki da ƴan uwa da masarautar Masakan dangane da taya shi murnan samun muƙamin tunda aka sanar har zuwa yanzu.

Wakilinmu ya binciko cewa ya daɗe yana tare da mai martaba sarkin Masaka kuma masarautar na matuƙar alfahari da shi game da irin gudunmawa da yake bayarwa a yankin da ma jihar baki ɗaya. Dalilin haka aka bashi wannan sarautar Ɗanmalikin Masaka wanda a cewar sa yake nufin mai tallafa wa fada.

By ukarofi