
Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ayyana Juma’a, 20 ga Fabrairu 2026, a matsayin ranar hutun aiki domin bai wa mazauna FCT damar shirin halartar zaɓen Ƙananan Hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu.
Haka kuma, Ministan ya sanar da takaita zirga-zirga a cikin Abuja daga karfe 8:00 na dare ranar Juma’a zuwa karfe 6:00 na yamma ranar Asabar. Ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su tabbatar da bin wannan umarni yadda ya kamata.
Wike ya yi kiran ne a wata sanarwa ta musamman ta hannun mataimakin sa na mussamman kan hudda da jama’a da kafafen sada zumunta Lere Olayinka, inda ya ƙarfafa al’ummar babban birnin da su fito da yawa su kaɗa ƙuri’a cikin lumana da bin doka.
Ministan ya ce an yanke waɗannan matakai ne da amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da tsaro da sauƙaƙa halartar zaɓen.
Ya kuma yi kira ga mazauna birnin da su mutunta ƙa’idoji da sakamakon zaɓe, yana mai cewa zaɓe nagari zai haifar da shugabanni masu inganci da za su ƙarfafa ci gaba, zaman lafiya da walwala a Babban Birnin Tarayya.
