Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sabbin manyan mataimaka na musamman da aka naɗa sun haɗa da Bishir Abubakar Kafin Soli daga ƙaramar hukumar Kankia.
Sai Hon Halilu Tanko Gilima daga ƙaramar hukumar Dandume sai Yusuf Abubakar Raɗɗa daga ƙaramar hukumar Charanchi.
Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ya taya waɗanda aka naɗa murna bisa samun wannan muƙami, tare da bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa za su taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cikar manufofin gwamnatinsa.
Ya buƙace su da su yi aiki daidai da ajandar sauyi ta “Gina Makomarku,” yana mai cewa rawar da za su taka na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da samun goyon bayan jama’a a matakin ƙasa da kuma cimma manufofin ci gaban jihar.
Malam Dikko ya kuma shawarce su da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, da masu tasiri a al’umma domin tabbatar da haɗin kai, ingantaccen wayar da kai, da ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen gwamnati a ƙananan hukumominsu.
Ya umurce su da su gudanar da ayyukansu cikin ƙwazo, aminci da kishin hidima, tare da kiyaye ƙa’idojin ladabi, haɗin kai, aiki tare, gaskiya, da rikon amana.
Wannan naɗi ya fara aiki nan take, yayin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da muhimman tsare-tsare domin inganta da ci gaban al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya.
