
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu, ya yi kira ga zaman lafiya da bin doka yayin zaɓukan da za a gudanar a Babban Birnin Tarayya Abuja da Jihar Kano da kuma Jihar Ribas a gobe Asabar.
Shugaban ya kuma buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da jami’an tsaro da kuma Hukumar Zaɓe, INEC, da su gudanar da ayyukansu cikin lumana da adalci.
Za a gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na FCT, da zaɓukan cike giɓi a mazaɓun Ahoada East II da Khana II a Ribas, sai jihar Kano da za a yi zaɓukan cike gurbi a ƙananan hukumomin Birnin Kano da Ungogo sakamakon rasuwar masu riƙe da kujerun a watan Disamba.
Shugaban ƙasar ya kuma shawarci masu katin zaɓe da su fito ba tare da tsoro ba, tare da gargadin jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji tashin hankali ko duk wani abu da zai lalata sahihancin zaɓe.
Kazalika, ya buƙaci INEC da ta tabbatar da sahihin tsari wajen tantance masu zaɓe da tattara sakamako, yana mai cewa gwamnati za ta tallafa wa duk wani yunƙuri na ƙoƙarin tabbatar da zaɓe mai ’yanci da tabbatar da adalci a jihohin.
