Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta mai kula da Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC) ta buƙaci shugabannin hukumar da su bai wa zuba jari a ɓangaren noma da tsaro muhimmanci na musamman yayin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2026.
Shugaban kwamitin, Sanata Titus Zam, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da mahukuntan NCDC suka bayyana gaban kwamitin domin kare kasafin kuɗinsu na 2026.
Bayan zaman sirri da aka yi da shugabannin hukumar, Zam ya ce kwamitin ya yi nazari kan dukkan abubuwan da ke cikin kasafin, inda ya gano cewa sun dace kuma suna da amfani ga yankin Arewa ta Tsakiya.
A cewarsa, kwamitin ya buƙaci hukumar ta fifita kashe kuɗaɗe bisa tanadin aikinta na musamman, domin al’ummar yankin su ga amfani kai tsaye daga ayyukan da za a gudanar, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware sun haifar da sakamako mai ma’ana.
Sanata Zam ya jaddada cewa aikin hukumar ba zai tsaya a sarari ba tare da cike giɓin da ke wasu muhimman ɓangarori na tattalin arziki ba.
Ya lissafa ɓangarorin da suka haɗa da noma, tsaro, lafiya, ilimi, gine-ginen jama’a da sauran ayyukan jinƙai da al’umma ke buƙata.
Ya ce yankin Arewa ta Tsakiya yanki ne da noma ya fi rinjaye, don haka wajibi ne a bai wa noma matsayi na gaba a cikin kasafin, abin da ya ce an riga an shigar da shi a tsarin kasafin 2026. Haka kuma, ya bayyana cewa hukumar na shirin haɗa gwiwa da kwararru a fannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, domin tallafa wa hukumomin tsaro su sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.
Sai dai ya nuna rashin gamsuwa kan yadda aka aiwatar da ɓangaren manyan ayyuka na kasafin 2025, yana mai cewa matsalar ba ta keɓanta da NCDC ba, illa wata ƙalubale ce da ta shafi aiwatar da kasafin a faɗin ƙasa baki ɗaya.
Kwamitin ya ce ya amince da jimillar naira biliyan 140 da aka gabatar a matsayin kasafin kuɗin NCDC na shekarar 2026, tare da ba da sahalewar amfani da kuɗin idan aka amince da shi domin amfanin yankin. Sanata Zam ya ce wannan shi ne matsayar kwamitin, yana mai fatan cewa kuɗaɗen za su taimaka wajen bunƙasa yankin Arewa ta Tsakiya.
