Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya bayyana cewa magoya bayansa za su mayar da martani idan har aka yi yunƙurin kaucewa ƙirga ƙuri’a su a zaɓen 2027.
A taron Obidient da ake gudanarwa a Uyo, jihar Akwa Ibom, Obi ya ce: “Idan a akwatin zaɓe na 2027 ba su ƙirga ƙuri’u ba, mu za mu ƙirga mutum.”
Maganar nan ta haifar da fassara daban-daban a shafukan yanar gizo da kuma a cikin harkokin siyasa. Wasu daga magoya baya sun bayyana cewa kalaman na nuni ne ga buƙatar tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓe, yayin da wasu suka yi gargaɗi cewa lafazin na iya zama mai tayar da hankali idan ba a fayyace ba.
Obi, wanda ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan Jihar Anambara, ya samu fiye da miliyan shida na ƙuri’u a zaɓen 2023, inda ya kammala na uku bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, amma ya samu babban goyon baya daga matasa da masu zaune a birane, musamman a Legas, Babban Birnin Tarayya, da yankin Kudu maso Gabas.
A cikin cakwalkwalin siyasa, Obi ya shiga jam’iyyar haɗaka ta ADC, inda ya bayyana shirin neman tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Wasu fitattun ‘yan siyasa da ke nuna sha’awar tikitin ADC sun haɗa da Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Ribas, da Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.
A ɓangaren hukuma, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ƙayyade ranar 20 ga Fabrairu, 2027, domin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya, yayin da zaɓen gwamnonin jihohi da na majalisun jihohi za a gudanar a ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa an tsayar da kwanakin ne bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka gyara), wanda ke buƙatar a gudanar da zaɓe ba a gaban kwanaki 150 ba ko bayan kwanaki 30 kafin ƙarshen wa’adin shugabanni a watan Mayu da Yuni 2027.
“Dangane da kundin tsarin mulkin Tarayyar Nujeriya na 1999 (da aka gyara), wa’adin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban aasa, gwamnonin jihohi da mataimakansu zai ƙare a ranar 28 ga Mayu, 2027, yayin da membobin majalisun tarayya da jihohi za su rushe a ranar 8 ga Yuni, 2027,” inji Amupitan.
