
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Asusun Tallafa wa Yara Ƙanana na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta sanar da cewa adadin yaran da aka yi wa rajistar haihuwa a Nijeriya acikin shekaru biyu da suka gabata ya ƙaru zuwa miliyan 14.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Mis Wafaa Saeed Abdelatef ta bayyana haka a yayin wata ziyara ga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Juma’a.
Ta yaba wa Uwargidan bisa jagorancinta na ba iya inda UNICEF take aiki ba, har ma a wuraren da rayukan yara ƙanana da iyalai suke amfana a sassan ƙasar.
Wafaa Saeed ta kuma bayyana godiyarta bisa jagorantar fannin da ya shafi rajistar haihuwa ga ƙananan yara ganin yadda ake samun nasara, tana mai yaba wa Oluremi akan gudumawar da take bayarwa.
A nata jawabin matar shugaban ƙasar, ta yi jinjina ga tasirin UNICEF a Nijeriya musamman ganin yadda shirin rajistar haihuwa ke bada damar yin rajista ga kowane ɗa a Nijeriya.
A cewarta, kowane yaro yana da ‘yancin zama ɗan ƙasa da kuma samun shaida a hukumance da zai taimaka masa wajen samun cancantar karɓar magani daga fannin lafiyar ƙasar.
Kazalika, ta yaba wa UNICEF bisa tallafa wa Nijeriya da yin alƙawarin cigaba da haɗa kai da hukumar wajen cimma nasarori a dukkan aikin da aka sanya a gaba a Nijeriya.
