Yadda wasu manyan ma’aikatu ke fama da ƙarancin kuɗi a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sabbin alƙaluma daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya sun nuna cewa manyan ma’aikatun da ke kula da muhimman ayyukan raya ƙasa na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, bayan an gano cewa ƙasa da Naira tiriliyan ɗaya ne aka saki domin ayyukan gwamnati a watanni bakwai na farkon shekarar 2025.

A wani rahoto da jaridar Newspoint ta wallafa, ta ce, binciken da aka yi kan bayanan kasafin kuɗi ya nuna cewa, duk da cewa an ware Naira tiriliyan 18.53 domin ayyukan jarin Ma’aikatun Tarayya da hukumomi a kasafin 2025, adadin da aka saki tsakanin Janairu zuwa Yuli bai wuce naira biliyan 834.80 ba. Wannan ya kai kashi 7.72 cikin 100 kacal na abin da ya kamata a kashe cikin watanni bakwai, inda aka samu giɓin kusan Naira tiriliyan 9.98.

Idan aka duba gaba ɗaya kasafin jarin 2025 da ya kai Naira tiriliyan 23.44, ana sa ran a kashe naira tiriliyan 13.67 zuwa watan Yuli, amma abin da aka kashe ya tsaya ne kan naira tiriliyan 3.60 kacal, abin da ke nuna giɓin kashi 73.7 cikin 100.

A cikin Takardar Tsarin Kasafi na Matsakaicin Lokaci (2026–2028), Ofishin Kasafin Kuɗi ya amince da raunin aiwatar da kasafin jarin, yana mai cewa jinkirin ya samo asali ne daga ƙoƙarin kammala tsawaita kasafin 2024 da aka miƙa har zuwa Disambar 2025.

A ɓangaren kuɗaɗen shiga kuwa, Gwamnatin Tarayya ta tara naira tiriliyan 13.67 daga Janairu zuwa Yuli, ƙasa da abin da aka yi hasashe na Naira tiriliyan 23.85. Kuɗaɗen mai sun gaza cika buri, duk da ƙaruwa a harajin kamfanoni da ɓAT.

Daga cikin naira biliyan 834.80 da aka saki domin ayyukan hukumomin gwamnatin tarayya, wannan ya kai kashi 6.1 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen shiga, kuma kusan kashi 4.1 cikin 100 na jimillar kashe kuɗin gwamnati da ya kai naira tiriliyan 20.40 a wannan lokaci. Haka kuma, daga cikin naira tiriliyan 3.60 da aka kashe gaba ɗaya a matsayin gwamnati, hukumomi sun samu kusan kashi 23 cikin 100 ne kawai, yayin da naira tiriliyan 1.68 suka fito daga rance na ƙasashen waje, lamarin da ke nuna dogaro da bashin waje.

Matsalar ta fi bayyana a manyan ma’aikatu. A Ma’aikatar Lafiya, daga cikin naira biliyan 218 da aka ware, naira miliyan 36 kacal aka saki. Ministan Lafiya, Muhammed Ali Pate, ya bayyana hakan a zaman kare kasafi, yana mai ɗora laifi kan matsalar kwararar kuɗi da tsaiko a tsarin gwamnati.

Haka zalika, Ma’aikatar Sufuri ta samu kusan kashi ɗaya cikin 100 ne kacal daga cikin naira biliyan 256.73 da aka ware mata. Ministan Sufuri, Saidu Ahmed Alkali, ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na ayyuka za a mayar da su zuwa 2026 saboda jinkirin sakin kuɗi.

A Ma’aikatar Ayyuka Ruwa da Bakin Teku, an saki naira miliyan 202 ne kawai daga cikin naira biliyan 3.53, wato kashi 1.7 cikin 100. Ministan ma’aikatar, Adegboyega Oyetola, ya ce ana tattaunawa domin cike giɓin, musamman ganin shirin bunƙasa tattalin arzikin ruwa.

A Majalisar Dokoki ta ƙasa, lamarin ya haifar da zazzafar muhawara, inda Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dattawa ya tambayi Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, kan dalilin ƙarancin sakin kuɗi. Shugaban Kwamitin, Sani Musa, ya soki tsarin “enɓelope budgeting,” yayin da Sanata Danjuma Goje ya bayyana halin a matsayin abin kunya.

Sai dai Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, ya kare kasafin 2025, yana mai cewa bambancin shiga da kashe kuɗi abu ne da ke faruwa a dimokuraɗiyya, kuma ana kan aiwatar da gyare-gyare domin daidaita al’amura.

Ga ministocin da suke aiwatar da ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wannan takurawar kuɗi na daga cikin manyan ƙalubalen tattalin arziki da gwamnatin ta fuskanta a 2025.

By ukarofi