Mai tsaron bayan Paris St-Germain, Achraf Hakimi ya ce zai fuskanci shari’a, bayan da wata mata ta zarge shi da yi mata fyaɗe.
Matar ta zargi kyaftin ɗin Morocco da yi mata fyaɗe a gidansa da ke babban birnin Faransa a shekarar 2023, lokacin tana da shekaru 24. Sai dai ya musanta zargin.
Ofishin mai gabatar da kara na Nanterre a yammacin birnin Paris, ya fara bincike a karon farko a watan Maris a 2023.
“A wannan lokacin zargin fyaɗe kawai ya isa a kai mutum gaban kotu,” inji Hakimi a shafinsa na ɗ.
“Wannan ba adalci ba ne ga wanda bai yi laifi ba, kamar yadda ba adalci ba ne ga waɗanda abin ya faru da gaske. Ina jiran wannan shari’a cikin natsuwa, wadda za ta ba da damar fito da gaskiya a bainar jama’a.”
Har yanzu ba a sanya ranar fara shari’ar ba.
An tuntuɓi ofishin mai gabatar da kara na Nanterre, domin jin ƙarin bayani.
Paris St-Germain za ta karɓi baƙuncin Monaco a wasan zagaye na biyu na cike gurbin zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba.
An haifi ɗan wasan mai shekara 27 a Sifaniya, amma ya zaɓi buga wa Morocco tamaula, kuma ya yi wasa 194 a Paris St Germain da lashe Champions League da Ligue 1 a kakar da ta gabata.
ƙoƙarinsa ya sa aka karrama shi a bikin Best FIFA Football Awards da aka gudanar a Paris, inda aka zaɓe shi cikin tawagar duniya ta ’yan wasa ta FIFPRO na shekara.
Moroko za ta kara da Scotland da Haiti da kuma Brazil a gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Amurka da Meɗico da Canada a wannan shekarar.
