Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Kasuwar Larabar Mata, Alhaji Umar Alasan ya jajentawa ‘yan kasuwar Singa bisa gobara da ta same su ‘yan kasuwar ya bayyana gobarar da cewa masifa ce babba da ta shafi kowa, domin Kano cibiya ce ta kasuwanci a ƙasar nan suna fata Allah ya mayar musu da alkhairi.
Ya yi kira ga shugabanni a matakin jiha da ƙasa da na ƙananan hukumomi da masu hali su duba su taimaka a ɗauki matakai kan dukkan abinda ke jawo faruwar gobara irin wannan a duba a gyara ayi kandagarki sannan kuma a tallafawa wanda suka gamu da asara a sanadin gobarar.
Ya ƙara da yin kira ga ‘yan kasuwa kasancewar ana cikin kusantowar watan azumi na Ramadan a sauƙaƙa kayayyakin masarufi don al’umma su saya a cikin rahusa da sauƙi i a sami walwala a samu a yi ibada cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Alhaji Umar Alasan ya yi kira ga yan kasuwa akan wannan gobara ta zama izina akan yan kasuwa su kula kowa ya sauke haƙƙin Allah dake kansa a kuma sassauta a tausayawa al’umma sai ubangiji ya kare musu dukiyarsu daga iftila.
Shugaban na kasuwar laraban mata yace Allah ya sawa kasuwar albarka, kudu da Arewa gabas da yamma al’umma na shiga cikinta sosai tana kuma cigaba da bunƙasa, kasuwa ce da suma tasowa suka yi suka sameta tun lokacinda turawa suke zuwa suna bada magani ga masu cutar kuturta kasuwar ta kafu.
Ya ce dalilin da yasa kasuwar ta ci sunan Larabar mata shine idan turawa sun zo suna bada magunguna sai mata dattijai da yan mata sukan kawo kayan gargajiya suna sayarwa tun daga nan ta sami wannan sunan.
Alhaji Umar Alasan ya ce a lokacinda suka karɓi shugabancin kasuwar sun zo sun tarar da matsaloli amma cikin ikon Allah sun shiga sun fita sun inganta tsaro a cikin kasuwar da fahimtar juna kuma jami’an tsaro na yan sanda dana sa kai da shugabancin kasuwa na bada gudummuwa don a zauna lafiya.
