’Yan Nijeriya 2,356 aka kora daga Indiya cikin shekaru biyar – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla ‘yan Nijeriya 2,356 ne ƙasar Indiya ta kora tsakanin shekarar 2019 zuwa 2024, a cewar rahotannin hukuma daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar.

Sabbin alƙaluma sun nuna cewa adadin korar ya ƙaru matuƙa a ’yan shekarun baya, inda aka samu ƙarin kusan kashi 333 cikin ɗari daga 339 a 2021 zuwa 1,470 a shekarar 2023–2024.

A tsakanin 1 ga Afrilu, 2023 zuwa 31 ga Maris, 2024, ’yan Nijeriya sun zama ƙasa mafi yawan mutanen da aka kora daga Indiya, suna wakiltar kashi 63 cikin ɗari na baƙi 2,331 da aka mayar da su ƙasashensu.

A matsakaici, kusan ’yan Nijeriya 122 ake kora duk wata – wato kimanin huɗu a kullum.

Ana fitar da korarrun ne ta ofisoshin rajistar baƙi na yankuna daban-daban a biranen Kolkata, Mumbai, New Delhi, Chennai, Amritsar, Bangalore da Hyderabad. Nijeriya ta zarce Bangladesh da Uganda a jerin ƙasashen da aka fi korar ‘yan ƙasarsu.

Rahotanni sun danganta yawan korar da laifukan wuce wa’adin biza da kuma safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar kula da yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Indiya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya 106 aka kama a 2024 bisa zargin safarar kwayoyi, abin da ya sa suka zama na biyu a jerin baƙi mafi yawan laifuka bayan Nepal.

A watan Disambar 2025, hukumomin Indiya sun kora ’yan Nijeriya 32 bayan wani samame da aka kai kan wata ƙungiya da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da halasta kuɗaɗen haram a birnin Delhi. Mutane 50 aka kama a jihohi da dama, yayin da wasu ke fuskantar shari’a.

A watan Afrilu 2025, majalisar dokokin Indiya ta amince da sabuwar dokar Shige da Fice da Baƙi ta 2025, wadda ta maye gurbin tsofaffin dokokin zamanin mulkin mallaka. Dokar ta tanadi hukuncin zaurin shekaru biyar ko tara mai tsauri ga duk wanda ya shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba ko ya wuce wa’adin biza. Haka kuma, ta wajabta wa cibiyoyin ilimi sanar da hukumomi bayanan ɗalibai ’yan ƙasashen waje – matakin da ake ganin ya ƙara tsaurara sa ido kan ɗaliban ƙetare, ciki har da ’yan Nijeriya.

Wannan yanayi na zuwa ne a daidai lokacin da alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki ke ƙarfafa tsakanin Nijeriya da Indiya. Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron G20 a New Delhi a 2023, inda ya gana da Firayim Minista Narendra Modi domin bunƙasa haɗin gwiwa a fannoni da dama. A 2024, Modi ya kai ziyara Nijeriya karo na farko cikin shekaru 17, inda aka karrama shi da lambar GCON. ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi uku, yayin da jarin Indiya a Nijeriya ya kai kusan dala biliyan 27.

Sai dai a ɓangare guda, matsin lamba na korar ‘yan Nijeriya na ƙaruwa daga Amurka, inda aka ƙara mutane 19 cikin jerin “masu aikata manyan laifuka” da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ke shirin kora. Hakan ya kawo adadin ‘yan Nijeriya da ake sa ran kora daga Amurka zuwa 113. Laifukan da ake zarginsu sun haɗa da cin zarafin ƙananan yara, zamba, safarar ƙwayoyi da halasta kuɗaɗen haram.

Hukumar ’Yan Nijeriya a ƙasashen Waje (NiDCOM) ta ce a shirye take ta karɓi duk ‘yan Nijeriya da aka kora, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Waje da sauran hukumomi domin tsara yadda za a tunkari lamarin.

Masana na ganin cewa yawaitar hijira da matsalolin tattalin arziki a gida na taka rawa wajen ƙaruwar ‘yan Nijeriya da ke neman rayuwa a ƙasashen waje, wani lokaci ta hanyoyin da ba su dace ba. Tare da sama da ‘yan Nijeriya 60,000 da ke rayuwa da aiki a Indiya – mafi girman al’ummar Afirka ta Yamma a ƙasar – alƙaluman korar na tayar da tambayoyi masu zurfi kan tsarin kula da ‘yan ƙasa a ƙetare, ɗabi’un al’umma da kuma ƙalubalen tattalin arziki a gida.

By ukarofi