
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin Iran sun sanar da naɗin Ayatollah Alireza Arafi a matsayin jagoran addinin ƙasar na riƙo kafin a zaɓi sabo.
Majalisar manyan malaman ƙasar mai mambobi 88 ce za ta zaɓi sabon jagoran addinin ƙasar.
Haka kuma al’ummar ƙasar ne suke zaɓar mambobin majalisar bayan kowace shekara takwas kamar yadda dokarsu ta tanada.
A ƙarƙashin dokokin ƙasar, waɗannan manyan malaman ne ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addini da zarar an rasa wanda yake kan muƙamin.
Saidai a halin yanzu ana ganin hakan zai yi wahala kasancewar babu kwanciyar hankali a ƙasar da ke cikin yanayi na yaƙi.
Ana cigaba da ruwan wuta a tsakanin Iran da kuma dakarun sojojin Amurka da Isra’ila, faɗan da ya ɓarke tun tsawon sama da kwana biyu, inda Iran ɗin ke luguden wuta a sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
