
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani jirgin yaƙin Amurka ƙirar F-15E ya yi hatsari a Kuwait yayin farmakin Iran a sansanin sojon saman Amurka, kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna.
Al’amarin ya faru ne a tsawon mil shuda daga sansanin Ali Al Salem.
An ga yadda jirgin ya ƙwace tare da nufin ƙasa a lokacin da yake ci da wuta ta ƙarƙashinsa.
Aƙalla ɗaya daga cikin matuƙa jirgin ya yi nasarar fita daga ciki ba tare da samun wani rauni ba, wanda ya samu agajin daga mazauna yankin.
Saidai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani akan mai kula da makaman ba.
Haka kuma, rundunar sojin Amurka ba ta fitar da wani saƙo a hukumance ba game da hatsarin.
Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta tabbatar da rukunin farko na waɗanda yaƙin ya shafa, inda ta sanar da mutuwar sojojinta uku da rauni da wasu biyar suka samutun farkon yaƙin, wanda aka fara tun a safiyar Asabar.
Shugaba Donald Trump naaura ya ci alwashin ramako ga sojojin da suka rasu a yaƙin, yana mai gargaɗin samun ƙarin asarar rayuka kafin yaƙin na haɗin-gwiwar Amurka da Isra’ila akan Iran ya ƙare.
Al’amarin ya faru ne yayin da yaƙin ya faɗaɗa, inda Isra’ila ta farmaki Labanon bayan Hezbollah sun harba makamai masu linzami a matsayin martani ga kisan Jagoran Musuluncin Iran, Ali Khamenei.
