
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matar marigayi jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, wato Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta rasu.
Marigayiyar ta rasu ne sakamakon munanan raunukan da ta samu a lokacin da Amurka/Isra’ila suka kai hari kan mijin nata.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da musayar wuta tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra’ila.
Tuni dai gidan talabijin na ƙasar Iran ya tabbatar da rasuwar Mansoureh Khojas Bagherzadeh maia shekaru 79 a duniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim ya ce Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta yi wata doguwar suma tun bayan harin da aka kai a ranar Asabar ɗin da ta gabata, wanda da ya yi sanadiyar mutuwar Khamenei.
Al’amarin ya faru ne yayin da ake cigaba da luguden wuta tsakanin ƙasashen a yankin Gabas ta Tsakiya.
