
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Iyalan ‘yar wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Ihotu John Rebecca, sun roƙi ‘yan ƙasa da su gaggauta kawo musu ɗauki sakamakon sace ta da aka yi a babban titin Benin.
‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da ita sun nemi a biya fansar Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa.
Rebecca matashiyar ‘yar wasa ce da ke buga wa ƙungiyar Pecesetter Queens FC a Gasar Premiership ta Nijeriya ta mata, wato NWFL, wadda aka yi awon-gaba da ita a lokacin da take kan hanyar koma wa gida.
Iyalan nata sun bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan wasan da ke bayar da gagarumar gudunmawa ga harkokin ƙwallon ƙafa na mata a Nijeriya.
A cewarsu, “Muna roƙon masu ruwa da tsaki a harkokin ƙwallon ƙafa, jagororin ƙungiya, masu ɗaukar nauyi, jami’an gwamnati, masu kula da wasanni da dukkan wani ɗan ƙasa da zai iya taimakawa.”
A yanzu dai hukumomi ba su tabbatar da al’amarin ba, yayin da ake ƙoƙari wajen ganin an sako ta.
