Zanga-zangar kisan Khamenei: Amurka ta soke alƙawuran biza a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya soke dukkan alƙawuran neman biza da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 4 ga Maris, 2026, sakamakon yiwuwar ɓarkewar zanga-zanga a Abuja dangane da rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Amurka da Iran.

A wata sanarwa da ofishin ya fitar, ya gargaɗi ’yan ƙasar Amurka da ke Babban Birnin Tarayya Abuja da su zauna a gidajensu, yana mai cewa akwai “babbar yiwuwar zanga-zanga” a birnin saboda rikicin da ke gudana da Iran.

Sanarwar ta fito ne bayan hare-haren sama na hazin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda aka kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Tehran.

Lamarin ya haddasa mummunar martani daga Iran, wadda ta harba makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha, ciki har da Saudiyya.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne da hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila a ƙarshen mako, kuma ya shiga rana ta biyar ba tare da alamun lafa ba. Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa lokaci ya ƙure wa Iran ta nemi sulhu, duk da alamu daga Tehran da ke nuna sha’awar tattaunawa a baya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce, “Sun rasa kariyarsu ta sama, rundunar jiragen yaƙi, rundunar ruwa da shugabancinsu. Suna son magana, amma na ce ‘ya makara!’” Ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren sun lalata muhimman cibiyoyi na Iran, yana mai cewa an yi hakan ne domin hana Iran fara kai hari.

Sai dai Iran ta musanta duk wata yiwuwar tattaunawa da Amurka. Wani babban mataimaki ga marigayi jagoran addinin, Mohammad Mokhber, ya ce babu wata tushe ta tattaunawa da Amurka, yana mai jaddada cewa Iran na iya ci gaba da yaƙi muddin ta ga dama.

A sakamakon yiwuwar zanga-zanga a Abuja, Ofishin Jakadancin Amurka ya sanar da soke dukkan alƙawuran neman biza na ranar Laraba, tare da alƙawarin tuntuɓar masu nema domin sake tsara sabbin ranaku. Ofishin ya buƙaci jama’a su riƙa bibiyar shafinsa na yanar gizo da kafafen sada zumunta domin samun ƙarin bayani.

Sanarwar ta kuma tunatar da cewa wasu zanga-zangar baya sun kai ga rikice-rikice tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a Nijeriya, abin da ya sa ofishin ya ɗauki matakin kariya domin lafiyar ’yan ƙasarsa.

By ukarofi