Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaban ƙungiyar Cigaban ‘Yan Kasuwa ta AMATA reshen kasuwar Singa da ke Kano, Alhaji Musa Ibrahim Na-Banki, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi adalci wajen tallafin da ake bai wa jihohi da suka fuskanci iftila’in gobara, musamman tsakanin Jihar Kano da Jihar Ogun.
Na Banki ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata addu’ar neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasar arziki da aka gudanar a kasuwar Singa, wadda Sarkin Kasuwar ya jagoranta.
A cewarsa, ‘yan kasuwar kasuwar Singa suna godiya ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa tallafin naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta bayar ga ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa, tare da kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa tallafin naira biliyan 3 da gwamnatin jihar ta bayar.
Ya ce tallafin da ɓangarorin biyu suka bayar ya kai naira biliyan 8, wanda a cewarsa abin a yaba ne kuma ya zo a daidai lokacin da ‘yan kasuwar ke cikin mawuyacin hali sakamakon gobarar da ta lalata kayayyaki da dama.
Sai dai ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi daidaito wajen raba tallafin, yana mai cewa Kano na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Nijeriya, kuma asarar da ‘yan kasuwar suka yi sakamakon gobarar ta kai maƙudan kuɗaɗe.
“A matsayin Kano na cibiyar kasuwanci mai dauke da miliyoyin al’umma, muna ganin ya dace a duba yadda ake raba tallafin domin a samu adalci tsakanin jihohi,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan kasuwar Kano sun yi asarar kayayyaki da darajarsu ta haura naira biliyan 25, don haka ya kamata a ƙara duba yiwuwar ƙarin tallafi domin farfaɗo da kasuwancin da gobarar ta shafa.
Na Banki ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa matakan da ya ɗauka na tabbatar da cewa an gudanar da rabon tallafin cikin gaskiya da adalci, tare da hana duk wani yunƙuri na yin magudi ko karkatar da kuɗaɗen tallafin.
Ya ce ‘yan kasuwar Kano suna goyon bayan gwamnatin jihar tare da nuna shirin ci gaba da ba ta haɗin kai wajen duk wani shiri da zai bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar.
A cewarsa, ‘yan kasuwa a Kano za su ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya a duk wani shiri da zai kawo ci gaba ga al’umma da kuma bunƙasar tattalin arzikin jihar.
Sai dai a ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban ƙungiyar AMATA na Jihar Kano, Alhaji Abdul’azeez Dalha Musa, kan batun da aka taso da shi, ya ce ba shi da wani ƙarin bayani a kai a halin yanzu.
