Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani mataimaki ga fitaccen mawaƙin Nijeriya Davido, mai suna Dre, ya janyo zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta bayan ya bayyana adadin kuɗin da yake ɗauka a matsayin “talauci” a rayuwarsa.
A wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, Dre — wanda ake dangantawa da tawagar DMW — ya ce idan ya buɗe asusunsa ya ga ƙasa da Naira miliyan 200, zai ɗauki kansa a matsayin wanda ya shiga matsin kuɗi.
A cikin salon magana na Pidgin, ya ce: “If like N200 million remain for my account, I go dey feel like say I don broke.”
Da aka tambaye shi ƙarin haske kan mafi ƙarancin adadin da zai sa ya ji daɗi, Dre ya sake jaddada cewa duk wani abu ƙasa da naira miliyan 200 a asusunsa na banki zai sa ya ɗauki kansa a matsayin wanda ya shiga matsin kuɗi.
Kalamin nasa ya haifar da ra’ayoyi mabambanta daga masu amfani da kafafen sada zumunta. Wasu sun bayyana cewa irin wannan furuci na nuna yadda wasu ke da bambancin fahimtar rayuwa da kuɗi, yayin da wasu kuma suka yi tsokaci cikin barkwanci, suna cewa idan suna da dubu hamsin a asusu, jin su suke kamar attajirai.
Wani mai sharhi ya ce idan manufar rayuwa ta taƙaitu ga tara kuɗi kawai, to akwai buƙatar a sake duba ma’anar nasara da cikawa a rayuwa. Wani kuma ya yi tambaya kan yadda za a sarrafa naira miliyan 200 cikin yanayin tattalin arzikin Nijeriya ba tare da tsari mai kyau ba.
Batun ya sake tayar da muhawara kan yadda masu kuɗi da mashahurai ke kallon wadata da talauci, musamman a ƙasar da mafi yawan jama’a ke fama da ƙalubalen tattalin arziki. Duk da cewa kalaman Dre na iya kasancewa a matsayin barkwanci ko nuna yanayin rayuwarsa, amma sun buɗe ƙofa ga tattaunawa mai zurfi kan kimar kuɗi da fahimtar wadata a al’umma.
