
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (DIG), Frank Mba tare da wasu manyan jami’an ‘yan sanda sun yi ritaya daga aiki a ranar Juma’a a ƙarƙashin hukumar yayin da ake sabunta shugabancinta.
Frank Mba, wanda ya kasance DIG dake kula da horo da ci-gaban jami’an hukumar a hedikwatarta da ke Abuja, ya yi ritaya daga aikin gwamnati bayan shafe shekaru 34 yana aiki.
Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda na ƙasar, Kayode Egbetokun, ya riga ya yi ritaya, yayin da sabon Inspector‑General of Police (IGP) Olatunji Rilwan Disu ya karɓi ragamar rundunar.
Mba tare da sauran jami’an na daga cikin waɗanda suka yi aiki a matsayin na hannun daman Egbetokun, wanda ya yi murabus a ranar 26 ga watan Fabarairu, 2026.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar kula da Harkokin ‘Yan sanda (PSC) ta gayyaci wasu jami’aiasu muƙamin mataimakin sufeto janar (AIGs) da ake shirin ƙara wa matsayi zuwa DIGs don cike guraben da suka samu bayan ritayar tsofaffin shugabannin.
Wannan mataki zai shafi manyan jami’ansu da dama yayin da ake ci-gaba da sabunta jagorancin rundunar.
Waɗanda aka gayyata sun haɗa da Margareth Ochalla, Kenechukwu Onwuemelie, Ishiaku Mohammed, Zacharia Fera Achinyan, Zango Ibrahim Baba, Mohammed Abdul Sulaiman, da kuma Umar Shehu Nadada.
Da yake jawabin bankawa a wata takarda, Mba ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa ba shi damar yi wa Nijeriya hidima a lokacin mulkinsa, yayin da ya bayyana farin cikinsa ga ‘yan ƙasa akan gudunmawarsu.
