Rasha na yi wa Iran leƙen asirin wuraren da sojojin Amurka suke, inji majiyoyi

Spread the love

Rahotanni daga majiyoyin leƙen asirin Amurka sun bayyana cewa ƙasar Rasha na bai wa Iran bayanan sirri game da wuraren da sojojin Amurkan suke da kuma motsin jiragen ruwansu da na sama, lamarin da ke nuna yiwuwar Moscow na shiga rikicin da ke gudana.

Majiyoyin sun ce yawancin bayanan da Rasha ke tura wa Iran na fitowa ne daga tauraron dan adam na leƙen asiri da ƙasar ke da su a sararin samaniya.

A gefe guda kuma, bayanan leƙen asiri sun nuna yiwuwar China na shirin tallafa wa Iran ta hanyar kuɗi, kayayyakin gyaran makamai da wasu sassan makamai masu linzami.

Saidai ana raɗe-raɗin cewa Beijing na taka-tsantsan saboda tana son a kawo ƙarshen yaƙin domin kada ya kawo cikas ga samar mata da makamashi, musamman man fetur daga Iran.

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce Rasha da Chana ba su taka muhimmiyar rawa ba a yaƙin da Amurka ke yi da Iran a yanzu duk da cewaan shiga mako na biyu ana gwabzawa.

By Babaji