
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Harkokin ‘Yan sanda PSC, ta amince da ƙarin matsayi ga wasu jami’ai bakwai daga na mataimakin sufeto janar mai daraja ta 1 (AIG) zuwa mataimakin sufeto janar mai daraja ta 2 (DIG).
Babban jami’in hulɗa da jama’a na (PSC), Torty Kalu ya bayyana haka a wata takarda a Abuja, ranar Juma’a.
Ya ce, an yi wa manyan jami’an ƙarin matsayin ne domin su cike guraben da wasu DIGs guda takwas suka bari a sakamakon ritaya da suka yi a kwanan nan.
Ritayar manyan jami’an ta bayar da damar naɗa Olatunji Disu, wanda AIG ne, a matsayin sabon sufeto janar na rundunar ‘yan sandan.
A cewar Kalu, an ƙara wa sababbin DIGs ɗin muƙaman ne bisa ƙwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu da kuma jarrabawa da aka gudanar ta rubuce da ta baka a ƙarƙashin jagorancin PSC, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙoƙarin hukumar wajen inganta shugabancin rundunar.
Waɗanda aka ƙara wa matsayin sun haɗa da Zachariah Achinyan, Zango Baba, Isyaku Mohammed, Margaret Ochalla, Mohammed Sulaiman, Kenechukwu Onwuemelie, da kuma Umar Nadada.
Mista Kalu ya ƙara da cewa, Shugaban PSC, Hashimu Argungu ya taya sababbin DIGs ɗin murna tare da kira a gare su da su ƙara hoɓɓasa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu domin ci-gaban ayyukan rundunar.
