
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Chana ta bayyana goyon bayanta ga Iran bayan naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar, inda ta ce wannan lamari na cikin gida ne wanda aka yi bisa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Jami’an gwamnatin Beijing sun jaddada cewa, ya kamata sauran ƙasashe su mutunta ikon mallakar ƙasar Iran tare da kauce wa tsoma baki a harkokin cikin gidanta.
Ƙasar Chanan ta kuma nuna adawa da duk wani barazana da ake yi wa sabon jagoran, tana mai kira ga kasashen duniya su mutunta cikakken ikon kasar Iran da kuma tsaron iyakokinta.
Wannan bayani dai ya zo ne bayan rasuwar tsohon Jagoran Koli na Iran Ali Khamenei, wanda rahotanni suka ce ya mutu sakamakon hare-haren da suka shafi rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila.
A halin yanzu kuma, ana ci gaba da musayar hare-haren soji a yankin, inda rahotanni ke cewa an kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki a wurare daban-daban.
Kazalika, Chana ta buƙaci bangarorin da ke rikicin su nuna haƙuri tare da rage tashin hankali domin kauce wa ƙara dagula tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan al’amari na cigaba da janyo hankalin duniya, yayin da ƙasashe ke sa ido akan yadda rikicin zai kasance a nan gaba.
