Manoma da makiyaya a Roni sun buƙaci tallafin gwamnati don bunƙasa noman rani

Spread the love

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano

Wasu manoma da makiyaya da ke gudanar da harkokin noman rani da kiwo a yankin ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa sun buƙaci Majalisar ƙaramar Hukumar da gwamnatin jihar da su ɗauki matakan bunƙasa harkokin noma da samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’ummar yankin.

Buƙatar ta fito ne daga bakin wani manomi kuma mai kiwo a yankin, Malam Nura Bala, wanda ya yi magana a madadin manoma ‘yan asalin yankin Roni.

Malam Nura Bala ya yi kira ga Majalisar ƙaramar Hukumar Roni karkashin jagorancin Shugaban ƙaramar Hukumar, Hon. Abba Ya’u, tare da kansilolinsa, da su duba halin da yankin ke ciki na rashin wadatattun ababen more rayuwa da ke taimakawa wajen bunkasa harkokin noma da rayuwar al’umma.

Ya bayyana cewa matasa su ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, don haka ya zama wajibi a samar musu da hanyoyin dogaro da kai ta hanyar inganta fannin noma da kiwo a yankin.

A cewarsa, yankin Roni na da wadatacciyar kasa mai kyau wadda za a iya noma amfanin gona iri-iri kamar alkama, tumatir da albasa, musamman a lokacin noman rani.

Sai dai ya ce babban kalubalen da manoman yankin ke fuskanta shi ne rashin madatsun ruwa da za su taimaka wajen samar da ruwan ban ruwa domin noman rani.

“Idan har gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, tare da gwamnatin karamar hukumar Roni, suka tallafa wajen samar da madatsun ruwa da sauran kayan aiki na noma, hakan zai taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin,” inji shi.

Baya ga harkar noma, Malam Nura Bala ya ce bangaren kiwon kaji da kifi na daga cikin sana’o’in da za su iya samar wa matasa dimbin ayyukan yi idan aka ba su kulawar da ta dace.

Sai dai ya koka kan tsadar abincin kifi da kaji, wanda ya ce na daga cikin manyan matsalolin da masu sana’ar ke fuskanta a halin yanzu, tare da cewa babu wani tallafi daga hukumomi da ke taimaka musu.

Saboda haka ya buƙaci gwamnati da ta kafa kwamiti na musamman wanda zai rika tallafa wa masu harkar kiwon kaji da kifi, tare da ba su shawarwari da horo domin inganta sana’ar.

Ya ƙara da cewa idan aka tallafa wa irin wadannan sana’o’i, za su taimaka matuka wajen rage zaman kashe wando a tsakanin matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin al’umma.

A ƙarshe, Malam Nura Bala ya bayyana cewa yana da burin ci gaba da taimakawa matasa a yankin ta hanyoyi daban-daban, musamman wajen karfafa musu gwiwa su rungumi ilimi da sana’o’i domin inganta rayuwarsu.

Ya kuma nuna fatan cewa gwamnati za ta duba bukatun al’ummar yankin tare da daukar matakan da suka dace domin bunkasa harkokin noma, kiwo da sauran sana’o’i a yankin Roni.

By ukarofi