Ba mu da alhakin rashin tura masu HND zuwa NYSC – JAMB

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta sake jaddada cewa, ba ita ce ke da alhakin shigar ɗalibai zuwa karatun Babbar Difloma ta HND ba, haka nan kuma ba ita ce ke da alhakin matsalolin da suke hana wasu masu wannan shaidar takardar samun damar shiga shirin hidimtawa ƙasa na NYSC ba.

Shugaban hukumar, Is-haƙ Oloyede, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ɗaliban Kwalejojin Kimiyya (NAPS) a ofishinsa, inda suka je domin tattaunawa kan matsalolin da ke addabar wasu ɗaliban kwalejojin kimiyya, musamman dangane da rashin samun damar shiga NYSC bayan kammala karatu.

A cewar Oloyede, JAMB ba ta da hannu a tsarin karɓar ɗalibai zuwa shirin HND a kwalejin kimiyya, don haka ba ta da bayanan da za su taimaka wajen tura su zuwa NYSC. Saboda haka ya shawarci ƙungiyar NAPS da ta kai ƙorafinta ga hukumomin da ke da alhakin kula da wannan fanni domin a nemo mafita.

Ya bayyana cewa aikin JAMB ya taƙaita ne ga shirya jarabawar shiga shirye-shiryen karatun digiri na farko, ƙaramin Diploma (ND) da kuma Takardar NCE, amma ba ta da hannu a harkokin shigar ɗalibai zuwa HND.

Shugaban ya ƙara da cewa, bayan ɗalibi ya kammala karatun ND, idan ya nemi shiga HND, to makarantar da zai shiga ce ke da cikakken ikon gudanar da shigar, domin JAMB ba ta da wani rawar takawa a wannan mataki.

Sai dai ya jaddada cewa JAMB na gudanar da tsarin shigar ɗalibai zuwa manyan makarantu ta hanyar wani tsarin kwamfuta mai suna: Central Admissions Processing System’ (CAPS), wanda aka ƙirƙira domin tabbatar da gaskiya da kuma inganta tsarin shigar ɗalibai.

Oloyede ya yi zargin cewa wasu makarantu na karya dokokin tsarin CAPS, inda suke shigar da ɗalibai ta hanyoyin da ba su dace ba. Ya ce duk wata shigar da aka yi ba tare da bin tsarin CAPS ba, to ba ta da inganci a idon doka.

Ya bayyana cewa tsarin CAPS ya taimaka wajen sauƙaƙa shigar ɗalibai, ya rage matsalolin da ake fuskanta a tsarin hannu, ya kuma bai wa ɗalibai damar samun cikakken bayani kan makarantu da shirye-shiryen karatu da ake da su.

Bugu da ƙari, ya ce tsarin yana faɗaɗa damar samun gurbin karatu, yana hana samun shigar makaranta fiye da ɗaya ga ɗalibi guda, sannan yana samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yanke shawara da gudanar da bincike a ɓangaren ilimi.

Oloyede ya kuma bayyana cewa wasu makarantu na gudanar da wasu shirye-shirye na karatu ba bisa ƙa’ida ba, musamman wasu nau’ikan HND na part-time, lamarin da ke sa NYSC ƙin amincewa da masu irin wadannan takardu domin shiga shirin bautar ƙasa.

Ya ce wasu daga cikin matsalolin da ɗaliban ke fuskanta na samo asali ne daga makarantu da ke kauce wa tsarin CAPS, suna shigar da ɗalibai fiye da adadin da NBTE ta amince da shi.

A cewarsa, irin wannan mataki na jawo rashin daidaito tsakanin masu takardar ND da kuma HND, musamman idan aka samu cewa sun yi karatun ne a makarantu daban-daban.

Shugaban ya shawarci makarantu da su bi dokoki yadda ya kamata domin kauce wa irin waɗannan matsaloli, yana mai bayyana cewa akwai wata polytechnic da ake fama da fiye da shari’o’i 42,000 na shigar ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba, wanda har yanzu makarantar ke ƙoƙarin magancewa.

A ƙarshe, Oloyede ya ce idan dukkan ɓangarori sun bi ƙa’idojin da aka gindaya yadda ya kamata, za a guje wa matsaloli, yana mai jaddada cewa JAMB za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da kuma hidima mai amfani ga duk masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

By ukarofi